Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya zargi kungiyar tsaro ta NATO da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, sai dai ya ce ba zai yi wat...
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya zargi kungiyar tsaro ta NATO
da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, sai dai ya ce ba zai yi watsi da kiran da ake yi na yin
Allah wadai da Rasha ba, a cikin kalaman da ke nuna shakku kan ko Ukraine ko
kasashen Yamma za su amince da shi a matsayin mai shiga tsakani.
Ramaphosa, wanda ke Magana a gaban majalisar dokokin kasar, ya ce da NATO
ta yi biyayya ga gargadin da aka yiwa shugabanninta tsawon shekaru da suka
wuce, musamman yadda take yunkurin fadadawa zuwa yankin gabashin Turai da yanzu
wannan yaki bai auku ba.
Shugaba Vladimir Putin ya kwatanta ayyukan Rasha a matsayin aiki na
musamman don karya ikon karfin wasu sojoji da kuma kawo karshen akidar ‘yan
nazi a Ukraine tare da magance abin da ya kira zaluncin NATO.
Ramaphosa ya kuma bayyana cewa, Putin ya tabbatar masa da kansa cewa
tattaunawar na samun ci gaba, amma ya ce har yanzu bai tattauna da shugaban
Ukraine Volodymyr Zelenskyy ba sai dai nan gaba.
Shugaban dai ya ce an
bukaci Afirka ta Kudu da ta shiga tsakani a rikicin Rasha da Ukraine, sai dai
bai bayyana wanda ya nemi ya sa baki ba.
No comments