Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matar Da Aka Sace A Jirgin Ƙasan Abuja Zuwa Kaduna Ta Haihu A Hannun Masu Garkuwa Da Ita

Daya daga cikin fasinjojin da 'yan fashin daji suka sace daga jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga wa...


Daya daga cikin fasinjojin da 'yan fashin daji suka sace daga jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.

Tashar talabijin ta AriseTV, wadda ta wallafa wannan labarin, ta kuma ce wani dan uwan matar ne ya sanar da su haka.

Dan uwa nata ya sanar cewa an kai wani likita wurin da ake rike da ita wanda ya taimaka mata wajen haihuwa.

"Matar na da tsohon ciki wanda ya kai wata takwas yayin da aka sace ta da sauran gwamman fasinjoji, kuma ta haihu ne bayan da 'yan ta'addan suka gayyaci likitoci su karbi haihuwar. Sai dai ba mu san halin da abin da ta haifa yake ba," in ji dan uwan matar.

A farkon wannan makon ne dai masu garkuwa da mutanen suka wallafa hotunan fasinjojin da kawo yanzu suka shafe wata guda cur a hannunsu.

No comments