Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sha’awarsa ga ilimi ta fito ne daga zuciyarsa. Atiku ya bayya...
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sha’awarsa ga ilimi ta fito ne daga zuciyarsa.
Atiku ya bayyana hakan ne bayan kaddamar da makarantar Atiku Abubakar ta ilimin zamantakewa da gudanarwa a jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ke jihar Kano a yau Laraba.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya ce kaddamar da wannan makaranta wani muhimmin abu na ziyarar da ya kai jihar.
Atiku ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Abin farin ciki ne na kaddamar da Makarantar Koyon Zamantakewa da Gudanarwa ta Atiku Abubakar a Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ke Kano a yau. Wannan kuma wani babban al'amari ne na ziyarata a Kano.
"Sha'awata kan ilimi ya fito ne
daga cikin zuciyata da kuma irin tasirin da hakan ya yi a tsawon rayuwata”,
inji shi.
Daga cikin wadanda suka
yi wa Atiku Abubakar rakiya akwai; mataimakin dan takarar shugaban kasa a PDP
din, Ifeanyi Okowa, Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan jihar
Sakkwato, Attahiru Bafarawa, Sanata Ibrahim Shekaru, tsohon gwamnan jihar
Jigawa, Sule Lamido da sauran su.
No comments