Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsalar Tabarbarewar Tarbiyya Iyaye Ne A Hakku Ba Gwamnati Ba - Sarkin Hausawa

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar tabarbarewar tarbiyar matasa a yau iyaye ne ke da laifi ba gwamnati ba, domin addini iyaye ne ya ...



Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar tabarbarewar tarbiyar matasa a yau iyaye ne ke da laifi ba gwamnati ba, domin addini iyaye ne ya dorawa hakki ba gwamnati ba, Sarkin Hausawan Paiko, Alhaji Rabi'u Na'taala ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da wakilin mu a Minna.

Nata'ala ya cigaba cewar babu wani hujja da mutum zai bayar gaban Allah kan lalacewar yayansa gaban Allah, domin yaya amana ce ga iyayensu.

Amma abin bakin ciki yau, sakamakon sakacin iyaye har ta kai yara matasa na aukawa jama'a da makamai, suna kisa suna sace sacen da ta kai wai wannan wata babbar matsala ce da ta kai masarauta mai daraja na soke wasu abubuwa masu muhimmanci saboda tsoron aukuwar fitina a lokuttan sallah, ya zama wajibi gwamnati da masarautar Minna su dauki matakin ba sani ba sabo ga duk yaron da aka samu da hannu a cikin ire-iren wadannan miyagun ayyukan.

Ta ya za a ce mutanen karkara ba su tsira ba, sannan mutanen gari ba su tsira saboda wasu tsirarrun yan daba da ba su wuce a murkushe su lokaci daya ba.

Ya kamata jami'an tsaro su tsaya kai da fata duk uban da aka kama dan shi yazo beli shi ma su cafke shi domin shi ne silar lalacewar dansa.

Da ya juya kan ayyukan gwamnati da ta somo, yace dole mu yabawa manomi gwamna Umar Mohammed Bago, domin tsarin da yazo da shi tsari ne da jihar ta dade tana bukata.

Yanzu ya samar mana da jami'ar ilimi a jiha cikin garin Minna, yanzu kuma ana kan batun jami'ar noma a garin Mokwa, sannan akwai batun jami'ar kiwon lafiya a garin Suleja.

Bayan duk layin da aka rutsa mafi yawa a jihar nan da yankunan kananan hukumomi ana kan aikin hanyoyi da magudanan ruwa wanda gwamnati ta sha alwashin samarwa guda dari biyar da ashirin da shida cikin shekaru biyu na mulkinsa.

Ya kamata duk wani dan siyasa in har da gaske yana son cigaban jihar nan, ya ajiye adawa a gefe daya ya marawa gwamnatin nan baya, amma maganar adawa a jihar Neja ba zai yi tasiri ba indai akan maganar aiki ne, domin gwamna ya nuna mana da gaske ya ke yi aiki yazo ba zaman dumama kujera ba.

Dukkanin ayyukan da muke gani a kasa ingantattu ne da za mu yi na'am da su.

Basaraken ya jawo hankalin makusantan gwamnan da su cigaba da taimaka ma shi, da ba shi goyon baya, domin nasararsa ta mu ce baki daya.


No comments