Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mutum Bakwai Sun Rasu Bayan Rushewar Gini A Abuja

  AÆ™alla mutum bakwai ne suka rasu sakamakon ruhsewar wani gini a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja. MuÆ™addashin darakta-janar na hukum...

 


Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu sakamakon ruhsewar wani gini a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Muƙaddashin darakta-janar na hukumar bada agajin gaggawa ta Abuja FEMA, Abdulrahman Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara wajen ginin da ya rushe a kan titin hanyar tafiya filin jirgin sama.

Ya ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar a sanadiyar wasu da suka shiga ginin, wanda hukumar kula da ingancin gine-gine ta Abuja take rusawa domin cire ƙarafa, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Ya ce bayan waÉ—anda suka rasu, akwai wasu mutum da suke jinya a asibiti, sannan ya gargaÉ—i mutane su guji jefa rayukansu cikin hatsari ta hanyar shiga cikin gine-ginen da aka rusa.

No comments