Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An shawarci gwamnatin Neja da ta dauki matakin kawo karshen matsalar ruwan sha a Minna

Daga Awwal Umar Kontagora   An shawarci gwamnatin Neja da ta gaggauta daukar matakin kawo karshen matsalar ruwan sha a Minna. Wa...

Daga Awwal Umar Kontagora 

An shawarci gwamnatin Neja da ta gaggauta daukar matakin kawo karshen matsalar ruwan sha a Minna. Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki a jihar Neja, Alhaji Muhammad Lawal Ibrahim ( Hamdala) ne yayi kiran laraban makon nan a Minna. 
Hamdala, ya cigaba da cewar akwai matsalar wutan lantarki da ya janyo masu fanfunan burtsatse da ke anfani da wutan lantarki yasa ba sa samun damar janyo ruwa, balle masu tura kuran ruwa su samu saukin samun ruwan da suke tallatawa a cikin unguwanni. 

Bayan wannan matsalar, akwai matsalar kamen da jami'an kula da shiga da fice ke yi, yasa da daman masu kokarin zuwa unguwanni masu nisa dan samo ruwan, dan saidawa, ba sa samun zuwa nesa dan samo ruwan saidawa saboda tsoron kamu. 

Tsakanin ranar talata zuwa laraba, muna sayen kuran ruwa akan naira dubu biyu, maimakon dubu daya da muke saye a baya. 

Ba mu hana gwamnati yin aikinta saboda samar da tsaro ba, amma akwai bukatar a samar da wata hanyar da al'umma zasu samu saukin rayuwa musamman akan ruwan sha, musamman a wannan watan na Ramadan da muke ciki. 

Dattijon, yace tabbas gwamna Umaru Bago, mutum ne mai sauraren koken jama'a kuma mai tausayi, ina jawo hankalin shi saboda ina da kwarin guiwar yana sane da wannan matsalar da muke ciki na matsalar ruwa a cikin garin Minna, dan haka muna kira da bada shawara ga maigirma gwamna Umaru Bago da ya taimaka ya samar mana hanyar da za mu samu saukin matsalar ruwa a garin Minna. 

Hamdala, ya jawo hankalin bakin haure, da su bi dokokin gwamnati musamman wajen tsalkake kan su daga zargin shigowa cikin kasar nan ba bisa ka'ida ba. 
Tunda sauran kasashe sun bar ECOWAS sun koma AES to ya zama wajibi kowa ya kiyaye dokokin kasa da kasa wajen kaucewa shiga hurumin da bai dace ba. 

Muna bukatar kulawa sosai , musamman a bangaren ruwa sha da kuma tausaya mana a matsayin mu na yan gudun hijirar siyasa da mu ka rasa muhallan mu a garuruwan mu da ya janyo tilasta mana dawo wa cikin garin Minna da zama.

No comments