Rundunar 'yan sanda a jihar Kano sun damke wasu matasa bisa zargin aikata laifin satar kayan 'yan kasuwa wadanda rushe-r...
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano sun damke wasu matasa bisa zargin aikata laifin satar kayan 'yan kasuwa wadanda rushe-rushen da ake yi a wasu sassan birnin Kano ya shafa.
Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na twitter ta ce 'yan sandan sun yi nasarar kama wadanda ake zargin ne sakamakon rahotonni da suka samu cewa na cewa daruruwan mutane sun taru suna shirin wawashe kadarori da kayan gine-gine a Triumph Plaza da ke karamar hukumar Fagge.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ana kan gudanar da bincike kan wadanda a ke zargin.
No comments