Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Lawal Ya Kai Ziyara NADDC, Ya Nemi Haɗaka Don Koyar Da Sana'o'i Ga Matasan Zamfara

A jiya ne gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ziyarci hedikwatar Hukumar Kula da ƙera motoci ta ƙasa (NADDC) da ke Abuja, inda...


A jiya ne gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ziyarci hedikwatar Hukumar Kula da ƙera motoci ta ƙasa (NADDC) da ke Abuja, inda ya nemi ƙarin haɗin gwiwa da alaƙa don samar da ayyukan dogaro ga matasa.

A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya samu tarba daga babban daraktan hukumar, Jelani Aliyu da manyan jami’an gudanarwarsa.

A hakan ya fito ne a wata sanarwar manema labarai da Sulaiman Bala Idris, Babban mataimaki na musamman (kan kafafen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a) ga gwamnan Zamfara ya fitar a ranar Laraba. 

Gwamna Lawal ya bayyana shirin gwamnatin jihar Zamfara na haɗin gwiwa da hukumar kula da ƙera motoci ta ƙasa (NADDC) domin koyar da matasan jihar sana’o’in da ake da buƙata domin dogaro da kai.  

"A yau, mun zo nan ne a matsayin wani ɓangare na ƙudirina na bibiyar duk wata dama da za ta ƙara wa jiharmu ta Zamfara tagomashi. Gwamnatina ta maida hankali ne ga ɓangarori irinsu tsaro, ilimi, noma, koyar da sana'o'i, da kuma ci gaban matasa.

“Na samu labarin cewa Hukumar NADDC ta gina Cibiyar koyar da matasa gyaran mota a Gusau, wanda har yanzu ba a ƙaddamar da ita ba. Gwamnatina za ta ba ku dukkanin goyon bayan da ya dace domin tabbatar da an ƙaddamar da cibiyar tare da gudanar da ayyukanta cikin sauƙi. Muna kuma fatan samun ƙarin haɗin kai da zai inganta Zamfara."

A na shi jawabin, Babban Daraktan hukumar ta NADDC, Jelani Aliyu, ya ce ziyarar da gwamna Lawal ya kai wani abin farin ciki ne da ke nuna cewa wannan sabuwar gwamnati a shirye ta shigo.

Ya kuma nuna jin daɗinsa ga gwamnan bisa bai wa hukumarsu damar da za ta sanya ranar da za a ƙaddamar da cibiyar koyar da matasa gyaran mota a Gusau.

Jelani ya ci gaba da bayanin cewa Cibiyar Horas da ƙera motocin ta ƙunshi kayayyakin aiki domin horaswa da kuma kayayyakin gyara na aikin injin mota. 

Kayayyakin da za a koya sana'a da su a cibiyar sun haɗa da na'urar ɗaga mota me ƙafa huɗu, na'urar ɗaga mota mai ƙafa biyu, na'urar da ake ɗora mota a kai, injin gyaran ƙarfen taya, na'urar cire taya, injin walda, kayan gwajin birki, injin cirewa da sanya noti, da sauran su. 

No comments