Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Har Yanzu Young Shekh Ya Ajiye Naira Miliyan Daya Ga Duk Wanda Ya Kawo Shaidar Ya Zagi Wani A Karatunsa

Daga Idris Umar, Zariya Young Sheikh yasa naira miliyan daya ga duk wanda ya kawo karatunsa da ya zagi wani malami a fadin kasar...


Daga Idris Umar, Zariya

Young Sheikh yasa naira miliyan daya ga duk wanda ya kawo karatunsa da ya zagi wani malami a fadin kasar nan.

A ranar da aka cika makil a wajen rufe tafsirin kur'ani da Young Sheikh ke gabatarwa a garin Zariya ta jihar Kaduna. 

A ranar Laraba 28 ga watan Ramadan, wanda ya yi daidai da 19 ga watan Afrilu 2023, Muhammad Zakir Shamsudin Ali Mai Yasin, wanda aka fi sani da Young Sheikh Zariya ya rufe tafsirin kur'ani mai girma na azumin da ya gabata. 

Kuma rufe tafsir din shi ne karo na uku da Sheikh din ya gabatar. 

Dimbin jama'a maza da mata yara da manya ne suka halarta. Malamai na addini da malamai daga manyan makarantun zamani da Sarakuna iyayen al'umma manyan gidajen jaridu a Nijeriya duk sun halarci wannan waje.

Bayan kammala karatun an yi tambayoyi, inda shi kuma Sheikh din ya bayar da amsa.

Young Sheikh dai karatuttukansa yana cikin wanda suke daukar hankali da kuma tattaunawa akai.

Sai dai bayan rufe tafsirin Young Sheikh ya kalubalanci duk wanda yake ganin shekarunsa ba su kai ya fara katatun Tafsirin ba. Young Sheikh ya ce mene ne hujjarsu akan hakan?

"A nawa tunanin abu biyu ne yasa masu wancan kalaman yasa suke yin kalamansu na farko dai shi ne don ba a cikinsu Allah ya tashe ni ba. Abu na biyu shi ne sun ji ina karanta Salatil-Fatihi wannan shi ne dalilansu bisa haka ina ba su shawara su hakura da ikon Allah", inji shi.

Young Sheikh ya kara da cewa; "wai wasu Malaman na zargina ina zaginsu a cikin karatuna to akan haka nasa Gidauniyyah ta ta ajiye naira miliyan daya ga duk wanda ya kawo shaidar na zagi wani malami a cikin karatuttukana tsawon shekaru uku da na fara", ya kalubalanta. 

Yana dai karatun bokonsa ne a makarantar Professor International Group of School dake Zariya.

Kuma shi ne na biyu a wajen mahaifinsa Malam Ali mai Yasin Garkuwan makarantar Zazzau.

Kuma yadda yake da hazaka a bangaren karatun Islama haka yake da hazaka a bangaren karatun zamani da ake cewa na boko. 

Young Sheikh ya sami horo ne a wajen mahaifinsa da mahaifiyarsa tun kafin shekarunsa sukai 10.

Shugaban makarantarsa Dakta Hamza Jibirul ya shaidi Young Sheikh da kyawawan dabi'a.

Tuni masarautar kasar Zazzau suka yi hani da kiran Young Sheikh da sunan yaro a kira shi da lakabin da Allah ya yi mishi.

No comments