Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a daren ranar Litinin ya gudanar da taron tsaro na farko na jihar a bayan fage a...
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a daren ranar Litinin ya gudanar da taron tsaro na farko na jihar a bayan fage a gidan gwamnatin jihar Katsina.
Taron majalisar tsaro ta jihar Katsina na farko a karkashin gwamnatinsa shi ne duba yanayin tsaro da kuma tsara dabarun ci gaba da dorewar zaman lafiya da ake samu a jiharmu.
Kwamitin ya hada da mataimakin gwamnan jihar Faruq Lawal Jobe; Sakataren gwamnatin jihar, Arch. Ahmed Musa Dangiwa; Shugaban ma’aikata, Jabiru Tsauri; Hakimin Rimi Alh. Aminu Abdulkadir, Wakilan Sojojin Najeriya, Rundunar ‘Yan Sanda, Ma’aikatar Tsaro, Hukumar Tsaro ta Civil Defence, Hukumar Shige da Fice ta Kasa, da Hukumar Kwastam ta Najeriya da dai sauransu.
Ofishin Babban Mataimaki na Musamman akan Kafafan Sadarwa Ga Gwamnan Jihar Katsina. 6/6/2023
📸 Isah Miqdad AD Saude
No comments