Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mista Husaini Gumel ya yaba wa wanda ya kafa kuma shugaban gamayyar jami'o'in MAAUN...
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mista Husaini Gumel ya yaba wa wanda ya kafa kuma shugaban gamayyar jami'o'in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa bayar da gudummawar motocin aiki guda biyu ga ofishin ‘yan sanda na Hotoro da ke cikin birnin Kano.
Gumel ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya kai ziyarar yabawar ga Farfesa Gwarzo wanda ta kasance shugaban gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo (AAG).
Ya ce maƙasudin ziyarar shi ne miƙa godiyar sa ga Farfesa Gwarzo bisa kyautar motocin aiki guda biyu ga ofishin ‘yan sanda na Hotoro wanda ya yi a kwanan nan.
Kwamishinan ƴan sandan wanda ya yaba da wannan karamcin, ya bayyana hakan a matsayin abin da zai ƙara musu himma wanda ya ce hakan zai taimaka matuƙa wajen inganta aikin ƴan sandan wajen gudanar da ingantacciyar aiki a yankin Hotoro da ma sauran wurare.
Gumel, wanda ya ƙara yabawa ƙoƙarin Farfesa Gwarzo, ya bada tabbacin cewa za a yi amfani da motocin yadda ya kamata tare da kula da su domin cimma burin da ake so.
Sai dai ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni a cikin al’umma da su ari irin karamcin Farfesa Gwarzo wajen ba ‘yan sanda tallafi irin wannan.
Da yake mayar da jawabi, Farfesa Gwarzo ya nuna matuƙar godiyarsa ga Kwamishinan ‘yan sandan bisa amincewa da gudunmawar da ya bayar, ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙulla alaƙa ta yadda za a inganta ayyukan tsaro a yankin da ma jihar baki ɗaya.
No comments