Daga Awwal Umar Kontagora Sakamakon ci gaba da amfani da makami wajen aukawa jama'a domin kwacen waya da yin sace sace da ma...
Daga Awwal Umar Kontagora
Sakamakon ci gaba da amfani da makami wajen aukawa jama'a domin kwacen waya da yin sace sace da matasan Minna ke yi wanda sanadin mutuwar mutane da dama da karya kananan 'yan kasuwa, wani uba kuma mazauni Minna Alhaji Musa Ibrahim ya nuna goyon bayansa ga gwamnatin jiha na bai wa jami'an tsaro damar bindige duk wani matashin da aka samu da makami don amfani da shi wajen aukawa jama'a.
Dattijon ya bayyana hakan ne a lokacin da wasu iyayen ke bukatar gwamnati tai zama da matasan don sulhuntawa da su, ya ce idan 'yan bindiga da suka hanawa al'ummomin karkara zaman lafiya, yanzu ana nufin an samu wasu yan ta'addar ne a cikin gari da dole su ma sai an zauna da su dan biya masu bukatun su. Ya kamata gwamnati ta dauki tsattsauran mataki don kawo karshen wannan lamarin, in aka yi sake wannan dabi'ar ya ci gaba abin da zai haifar gwamnati ba za ta iya shawo kan shi ba.
Ya ce; "Babu wani dalilin da zai sa a mutunta dan ta'adda, domin matsayinsu daya da wadanda ke cikin dazuka suka hana zaman lafiya, wajibin gwamnati ne kare rayuka da dukiyoyin jama'a, duk wanda ya ce zai zama barazana ga zaman lafiya dan ta'adda ne dole ne a dauki mataki akan sa".
Alhaji Musa Ibrahim, ya kara dacewar wajibin iyaye ne su rika zama suna bai wa 'ya'yansu shawarwari na gari ta hanyar kulawa da tarbiyarsu, da nusar da su muhimmancin riko da sana'a, amma barin yara kara zube suna aikata abubuwan da ransu ya ba su ba zai haifar da da mai ido ba.
Matsalar sara suka da aukawa jama'a zama ruwan dare a Minna fadar gwamnatin jiha wanda ya yi sanadin salwantar rayukan jama'a da dama, yayin da wasu ke fama da jinya sakamakon raunukan da yan sara sukan sukai masu.
Ko a satin da ya gabata dai, an tsinci gawar wani bawan Allah kwance cikin gini a gefen rukunin gidajen M. I. Wushishi daura da hanyar Aloe-vera cikin garin Minna, rahotanni sun tabbatar da salwantar da ran wani dan kasuwa da ya fito daga kasuwar Paiko, inda mai ya karewa motar haya da yake ciki, yayin da suke jiran direban motar wasu gurbatattun matasa suka auka masu inda suka soka masa tsinken karfe sai da ya fito a kirjin shi wanda hakan ya yi sanadin rasa ransa.
Gwamnatin jihar Neja dai ta bai wa jami'an tsaro umurnin harbe duk wani matashin da aka samu dauki da mataki yana yawo cikin jama'a.
Wanda duk da wannan umurnin dai har yanzu ana samu rahotannin hare haren matasan a wasu unguwanni, wanda kusan ya jefa 'yan kasuwa da ke cikin unguwanni suna sana'a fargaba da tsoron yadda matasan ke shigowa suna hargitsa jama'a suna sace sace a shagunan al'umma.
No comments