Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Na Son A Kafa Rundunar Bai-Ɗaya Domin Yaƙar Ta'addanci A Afirka

  Nijeriya ta bayyana buƙatar gaggawa ta ganin Cibiyar murƙushe ta'addanci a Afirka ta kama aiki gadan-gadan a ƙoƙarin dukkan masu ruwa ...

 


Nijeriya ta bayyana buƙatar gaggawa ta ganin Cibiyar murƙushe ta'addanci a Afirka ta kama aiki gadan-gadan a ƙoƙarin dukkan masu ruwa da tsaki a nahiyar na kawar da ta'addanci.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce lallai bai kamata ƙasashen Afirka su yi biris da tunanin kafa wata rundunar ko-ta-kwana a nahiyar ba, wadda ayyukanta za su haɗar da tunkarar ta'addanci.

Ya bayyana haka ne yayin buɗe wani babban taron wuni biyu don ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe Afirka da bunƙasa cibiyoyin gwamnati, don shawo kan matsalolin ta'addanci.

Kasashen Afirka dai musamman na yammaci na fama da matsalar tsaro da ke haddasa rasa dubban rayuka da tilasta miliyoyi barin muhallansu.

Masana fannin tsaro na yi wa taron na Abuja kallon wani ɗan-ba da za a dasa wanda ka iya samar da bakin zare ga matsalar da ke ci wa yankin tuwo a kwarya.

No comments