Hoto: Shugaban ƙungiyar Ciyamomin Nijeriya kuma Slshugaban ƙaramar Hukumar Lafia, Alhaji Aminu Ma'azu Maifata Daga Zubairu M...
Daga Zubairu M. Lawal Lafia
Samarwa Sarakuna da gurbin aiki a tsarin mulki zai ƙara tabbatar da zaman lafiya a tarayyar Nijeriya.
Shugaban ƙungiyar Ciyamomin Nijeriya (Algon President) kuma Shugaban ƙaramar Hukumar Lafia ta jihar Nasarawa Alhaji Aminu Ma'azu Maifata ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Lafia.
Aminu Ma'azu Maifata ya ce; tun ina mataimakin Shugaban Ciyamomi na ƙasa nake bada shawarar shigor da Sarakuna cikin tsarin Gwamnatin ƙasa.
A yanzu da na zama Shugaban Ciyamomi na ƙasa wato (Algon president) na taso da wannan ƙudurin, saboda ina da tabbacin Sarakuna suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce a don haka ne yake da burin ganin cewa an aamar masu da gurbi cikin gwamnati domin gudanar da aikin da zai haɗa kan al'umma da tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce; duk shugaban ƙaramar hukuma yana fatan ya ga an tabbatar da wannan ƙudurin saboda Sarakuna suna taimakawa shugabannin ƙananan hukumomi da shawarwari na ci gaba a kowanne ɓangare musamman idan ana buƙatar zaman lafiya.
Maifata ya ce; a ranar Asabar a jihar Nasarawa kowa ya ga yadda sarakuna suka nuna haɗin kai sun dunƙule waje guda a bikin murnar cika shakaru biyar na Sarkin Lafia kan gadon mulki.
"Babu sassa a faɗin ƙasarnan da Sarakuna ba su zo ba", in ji shi. Aminu Ma'azu Maifata ya yaba da salon Sarautan Mai Shari'a Sidi Bage.
Ya ce; shekara biyar da Mai Shari'a Sidi Bage Muhammad ya yi kan gadon sarautan Lafia an samu ci gaba sosai.
"Lokacin da aka zaɓe shi a matsayin Sarki ina shugaban ƙaramar Hukumar Lafia. An gudanar da zaɓe babu musgunawa babu tilastawa saboda gwamnati bata da Ɗan takara ta bar masu zaɓen Sarki su zaɓi wanda suke so. Waɗanda suka zaɓi Sarkin sun roƙi Gwamnati ka da ta canza musu wanda suka zaɓa", ya labarta.
Ya ci gaba da cewa; ko da ya hau kujerar mulki bai bai wa jama'a kunya ba. Abin da ake tsamnani na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba an gani a gare shi.
"Ya haɗa kan al'ummar Lafia kowacce ƙabila baƙo da ƴan gari, kowa na yabon Sarki Sidi Bage.
"A matsayina na shugaban ƙaramar Hukumar Lafia, ina jin daɗin zama da Sarki Sidi Bage. Saboda duk da matsayin shi na Uba a gare ni amma duk inda zai yi tafiya cikin jihar ko wajen jihar sai ya sanar da ni. Idan nabce ai wannan babu damuwa sai ya ce a'a ai doka ne ta ce haka. Shi kuma mai bin doka ne.
"Kuma duk abin da zamuyi da ya shafi ci gaban ƙaramar Hukumar Lafia za ka tarar da shi ya shigo shi ne gaba-gaba.
"Haka ma baya wasa da batun maganar zaman lafiya, yana haɗa kan Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni da masu faɗa a ji. Kai har ranar dokar tsaftar muhalli na ƙarshe wata Sarki na zaga gari ya tabbatar jama'a sun tsaftace muhallinsu.
"Hata ƴan kasuwarmu na garin Lafia da masu koyon sana'a Sarkin na ƙoƙarin ya ga ci gabansu. Yanzu haka Sarki ya yi ƙoƙari an kawo mana makarantar koyon sana'a a ƙaramar Hukumar Lafia an kawo kayayaki komai da komai. Mu kuma ƙaramar Hukumar mun ba da fili ana ginawa a Akunza" ya jaddda.
Daga ƙarshe (Algon President) ya yi kira ga al'ummar ƙaramar Hukumar Lafia da su ci gaba da adu'o'i na alheri ga Sarkin Lafia Mai shari'a Sidi Bage.
Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar Nasarawa da su ci gaba da bai wa Gwamna Abdullahi Sule goyon baya domin ci gaban jihar Nasarawa.
Ya ce; dole al'ummar jihar Nasarawa su yabawa Gwamnatin Abdullahi Sule saboda ayyukan alheri da yake gudanarwa a kowacce ƙaramar Hukuma da Lafia babban birnin jihar.
No comments