Abdulrasheed Bawa Daga Muhammad Farouk Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da sunan Abdulrasheed Bawa tare da aika sunan na shi g...
![]() |
Abdulrasheed Bawa |
Daga Muhammad Farouk
Shugaban
kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da sunan Abdulrasheed Bawa tare da aika sunan
na shi ga Majalisar Dattawan Nijeriya domin tabbatar da shi a matsayin shugaban
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC.
A wata
takarda da shugaban kasar ya aikawa shugaban majalisar Dattawan, Ahmad Ibrahim
Lawan, shugaban ya ce ya yi hakan ne duba da sashen doka na 2(3) na 1, CAP E1
na dokar EFCC Act 2004 kamar yadda Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya
tabbatar a sanarwar da ya fitar a yau Talata 16 ga watan Fabarairun 2021.
Bawa, mai
shekara 40 a duniya, ya kasance kwararre ne wajen bincike sannan yana da basira
a harkar abin da ya shafi binciken almundahana, rashawa, cin hancin jami’an
gwamnati, halasta haramtattun kudi da sauran miyagun laifuka da suka shafi
tattalin arziki.
Femi
Adesina ya ce; Bawa ya samu horo na musamman a sassan duniya daban-daban, kuma
yana daga cikin ma’aikatan EFCC na farko a 2005.
Bawa
yana da digirinsa na farko a bangaren tattalin arziki, inda ya kuma ya yi
digirinsa na biyu a bangaren huldar Jakadanci da diflomasiyya.
Allah ya sa zai iya aikin ba tsoro ba sonki. In almundahana ta koma ta na'ura zamani yan zamani ya kamata su yi bincike. Hausawa na cewa "karen bana shike maganin zomon bana"
ReplyDelete