Daga Awwal Umar Kontagora Rundunar Barikin Sojoji na Zuru wato 223 Light Battalion, Zuru tayi nasarar dakatar da wani harin da w...
Daga Awwal Umar Kontagora
Rundunar Barikin Sojoji na Zuru wato 223 Light Battalion, Zuru tayi nasarar dakatar da wani harin da wasu ƴan ta'adda suka kai garin Ribah, hedkwatar karamar hukumar mulki ta Danko-wasagu da ke jihar Kebbi:
Yan ta'addan wanda adadin su ya kai sama da mutane 400 sun yi yunkurin kai harin ne ranar laraba 9/7/2025.
Jami'an sojin sun yi musayar wuta da ta'addan wanda hakan ya baiwa jami'an sojin nasarar hallaka wasu ƴan ta'addan da dama inda wasu kuma suka tsere da gawarwakin ƴan uwansu ƴan ta'addan inda kuma suka bar wasu gawarwakin da kuma makaman waɗanda aka kashe.
Daraktan harkokin tsaro na ofishin mataimakin Gwamnan jihar Kebbi wato Malam Abdul Rahman Zagga ne ya tabbatar da faruwar hakan a garin Birnin Kebbi a lokacin da yake wata zantawa da manema labarai.
Zagga ya yabawa jami'an tsaron bisa wannan kokari da suka yi wajen dakatar da wannan harin.
Haka kuma ya yabawa jami'an sojin sama bisa suma irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar wannan bata kashin da aka yi tsakanin ƴan ta'addan da jami'an sojojin.
Sojin saman sun taimaka sosai wajen hallaka dukkanin ƴan ta'addan da suka gudu zuwa cikin daji tare da kuma raunata wasu da dama.
Haka kuma ya bayyana cewar duk da harin da suka kawo tun a farko tare da harbe-harbe ya razana al'ummar garin da dama, yanzu an samu kwanciyar hankali bayan da sojojin suka samu wannan gagarumar nasarar.
Zagga ya ƙara da cewar, ana zargin wannan ƴan ta'addan sune suka addabi wani ɓangare na jihar Neija wanda yanzu kuma suka shigo jihar Kebbi.
A wata mai kama da wannan kuma jami'an sojojin barkin sojan Dukku Barack dak e cikin garin Birnin Kebbi sun yi nasarar dakatar da wani hari da ƴaƴan kungiyar lakurawa suka kai garin Mera da ke ƙaramar hukumar mulkin Augie.
Yan ta'addan na lakurawa sun kai harin ne domin satar shanu a garin na Mera inda jami'an tsaron soji suka tarwatsa su wanda hakan yasa suka gudu.
Abdulrahman Zagga ya bayyana cewar gwamna Dakta Nasir Idris yayi farin ciki da wannan nasarar da sojojin suka samu tare da yi musu godiya da jinjina ta musamman dama sauran jami'an tsaron da suka taimaka wajen samun wannan nasarar.
Haka kuma ya bayyana cewar gwamna ya ƙara jaddada kuɗurinsa na cigaba da taimakawa jami'an tsaro wajen samar da ingantaccen tsaro a fadin jihar.
Abdulrahman Zagga ya kuma bayyana irin nasarar da jami'an tsaro suka samun a satin da ya gabata wajen kuɓutar da wasu mutane shida (6) da ƴan ta'adda sukayi garkuwa da su da kuma kwato wasu dabbobin da aka sace
No comments