Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Bello Matawalle da hadin gwuiwar kungiyoyin ta...
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Bello Matawalle da hadin gwuiwar kungiyoyin tallafin kiwon lafiya USAID sun kaddamar da rabon maganin zazzabin cizon sauro na shekara ta 2021 ga yara “yan kasa da shekaru biyar da ke fadin jihar.
Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya na jihar Zamfara, Dk. Habibi Yalwa,ya bayyana cewa, sun kaddamar da maganin sama da miliyan hudu ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar a fadin jihar don dakile yaduwar cutar zazzabin cizon sauro da ke yaduwa a farkon damuna.
Dk. Habibi Yalwa ya kara da cewa, tunin maganin cizon zazzabin sauro ya isa a cibiyoyin kiwion lafiya da ke karkara da birane, lunguna da sakon cikin jihar.kuma maganin zazzabin cizon sauro ana shan shi ne sau uku a jere a cikin wata daya har na tsawo wata hudu za a samu karin bayani daga ma’aikatan masu bada maganin.
Tunda farkon taron kaddamar da maganin, Dk. Aliyu Muhammad Mai kiyo, Sakataren zartarwar na hukumar kula da bada magani na jihar Zamfara, shine ya gabatar da jawabin maraba ga baki sai kuma Dk. Samsu Bello, Shugaban shirin yaki da cutar zazabin cizon sauro na jihar, ya gabatar da jawabin godiya ga wadanda suka halarci bikin kaddamar da bada maganin zazzabin cizon sauro.
No comments