Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Gwarzo Ya Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Sunan Alhaji Aminu Dantata a Jami’a Don Karramawa

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda ya kafa rukunin jami’o’in MAAUN, ya roƙi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta girmama marigayi...

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda ya kafa rukunin jami’o’in MAAUN, ya roƙi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta girmama marigayi ɗan kasuwa kuma dattijo a ƙasa, wato Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ta hanyar saka sunansa a ɗaya daga cikin jami’o’in da ke yankin Arewa maso Yamma.

Farfesa Gwarzo, wanda ya bayyana wannan buƙata a ranar Laraba, ya ce saka sunan Dantata a jami’a a yankin zai kasance abin yabo matuƙa, la'akari da gagarumar gudummawar da ya bayar wajen ci gaban ilimi a rayuwarsa.

"Ina kira ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta girmama marigayi Alhaji Aminu Dantata ta hanyar saka sunansa a ɗaya daga cikin jami’o’in da ke yankin, duba da irin gudummawar da ya bayar musamman ga fannin ilimi," in ji Farfesa Gwarzo.

Ya bayyana cewa irin wannan mataki ne kawai zai sa a ci gaba da tuna kyautatawar Dantata a harkar ilimi har abada, sannan kuma hakan zai zamo abin koyi ga wasu da kuma waɗanda ba a haifa ba.

Farfesa Gwarzo ya bayyana kyautatawar Dantata a fannin ilimi a matsayin na musamman, inda ya ce akwai buƙatar a yaba masa da irin sadaukarwa da gudummawar da ya bayar a fannin ilimi, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan alheransa da za a riƙa tunawa da shi. 

"Dantata ya zuba jari sosai a fannin ilimi – ya bayar da kuɗi da gine-gine ga makarantu daban-daban. Ta hanyar gidauniyarsa ta Dantata Foundation da wasu shirye-shirye, ya tallafawa ɗalibai marasa galihu domin su yi ilimi. Haka kuma, shi ne shugaban jami’ar Al-Qalam Katsina na farko da aka naɗa," in ji shi.

Wannan masani a fannin ilimi da kasuwanci, ya bayyana Dantata a matsayin gwarzon mai bayarwa ta fuskar jin ƙai, inda ya ce Dattijon marigayin zai ci gaba da kasancewa abin tunawa da nuna ƙauna saboda manyan gudummawarsa ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙin Nijeriya da ma yankin Yammacin Afirka gaba ɗaya.

"Saboda haka, karrama marigayi Dattijon ƙasa da wannan girmamawa zai kasance abin maraba da yabo daga dukkan waɗanda suka ci moriyar jin ƙansa da kuma wasu da dama," in ji Farfesa Gwarzo.

No comments