Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Osinbajo Da Mutane Dubu 16 Za Su Halarci Bikin Mika Sandar Mulki Ga Sarkin Kano

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari na daga ci...



Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari na daga cikin manyan baki da za su halarci mika sandar Mulki ga Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Bikin bada sandar da aka tsara gudanar da shi a filin wasa na Sani Abacha ranar Asabar 3 ga watan Yuli, ana saran mutane dubu 16 ne zasu halarta.

Aminu Ado Bayero, wanda shi ne Sarki na 15 a masarautar Kano, an nada shi ne a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020 bayan gwamna Abdullahi Ganduje ya cire Sarki Muhammadu Sanusi na II.

Yayin da yakewa manema labarai karin haske kan bikin, Dan-Dakan Kano, Abbas Dalhatu ya ce za a yawaita jami’an tsaro a bikin.

Ya ce jami’an tsaro dubu 4 ne da suka hada da Yan sanda, DSS, Sojoji da na Civil Defence zasu halarci bikin.

Abbas Dalhatu ya yi bayanin cewa, an bawa marigayi Alhaji Ado Bayero Sandar girma a filin wasa na Sani Abacha shekaru 53 da suka wuce sannan za a bawa dansa a irin wurin a yanzu.

“Zamu karbi baki da dama ciki har da mataimakin shugaban kasa, Sarakuna da sauran su”, inji shi.

Sannan ya kara da cewa, Sarkin zai yi hawa a ranar Litinin domin zagaya birnin Kano.

No comments