Sarkin kasar Tiv wanda aka fi sani Tor Tiv of Tiv, Farfesa James Ortese Ayatse, ya jinjinawa shugaba kuma mu’assasin Jami’ar Maryam ...
Sarkin
kasar Tiv wanda aka fi sani Tor Tiv of Tiv, Farfesa James Ortese Ayatse, ya
jinjinawa shugaba kuma mu’assasin Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN),
ta Nijeriya dake Kano bisa kafa jami’ar tare da samar mata da kayan aiki na
zamani.
Sarkin
gargajiyar ya jinjinawa Farfesa Gwarzo ne a yayin da ya kai ziyara a jami’ar
dake Hotoro a cikin kwaryar Kano da yammacin ranar Juma’a.
Sarkin
kuma shugaban al’umma, an jagorance shi inda aka zagaya da shi tsangayoyin jami’ar
daban-daban tare da sassan jami’ar, dakunan karatu, wuraren bincike, ajujuwan
karatu, ginin gudanarwa na jami’ar, ofisoshi dake cikin jami’ar, inda ya yabawa
wanda ya samar da jami’ar bisa wannan himma da kokari.
“na yi matukar jindadi da wannan tsarin. Na yi
farin ciki bisa yadda na ga gine-ginen da aka yi. Suna da aiki da nagarta”,
inji Sarkin.
Har
wala yau Basaraken ya shawarci hukumar gudanarwa na jami’ar da su kafa cibiyar
sadarwa da fasahar zamani domin taimakawa jami’ar wajen samun karbuwa, ingancin
dalibai tare da kuma hanyar bunkasa koyarwa da bincike.
Sannan
ya nemi wanda ya kafa jami’ar ta MAAUN da ya ci gaba da maida hankali bisa kyawawan
tsare-tsaren da ya shimfida musamman wajen bunkasa tsarin tare da ci gabantar
da bangaren ilmantarwa da kuma kayayyakin da aka sanya.
“a matsayina na Basarake kuma Farfesa da yake
da masaniya wajen gudanar da jami’a, na yi matukar jindadi da abin da na gani”,
ya tabbatar.
Ya
kara da cewa; “a don haka, akwai bukatar samar da kudaden da za a ci gaba da
kyawawan ayyukan da aka faro domin gudun tsayawar aikin”, ya lurantar.
Ya
yi alkawarin bayar da duk wata dama a kowanne lokaci domin yin lurantarwa da
kuma bayar da shawara a muhimman abubuwan da jami’ar ke bukatar mayar da
hankali a kai tun farko don ba ta damar cimma nasarar da ake bukata.
Honorabul
Prince Moses Ternenge yana daga cikin wadanda suka raka Basaraken Farfesa
Iorzua Ortese James Ayatse a ziyarar da ya kai jihar Kano.
Basaraken
ya ce ya zo ne Kano ne domin halartar taron nadin sarauta ta Sarkin Kano,
Alhaji Aminu Ado Bayero, inda ya yanke shawarar duba abin da ke gudana a wannan
jami’ar ta duniya.
No comments