Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari -Hakan ya lalata kasuwancinmu, inji wani dan kasuwa Daga Ammar M. Rajab Al’ummar jihar Katsina...
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari |
-Hakan ya lalata kasuwancinmu, inji wani dan kasuwa
Daga
Ammar M. Rajab
Al’ummar
jihar Katsina mazauna kananan hukumomin da yanke sadarwa ya shafe su sun yi
kira ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da Hukumar sadarwa ta
Nijeriya, NCC da sauran hukumomin tsaro da su dubi Allah su dawo musu da
sadarwa a jihar domin a cewarsu hakan ya kuntata rayuwarsu tare da dakile ci
gaban harkokinsu.
Al’ummar
sun koka ne a yayin zantawarsa da MADOGARA a yau Litinin, inda suka
shaidawa wakilinmu cewa duk da datse sadarwar da aka yi hakan bai hana ‘yan
bindigar ci gaba da kai hare-hare da kuma garkuwa da jama’a ba.
Jihohin Sakkwato da Kaduna tuni suka dawo da sadarwar bayan da farko an datse, a yayin
da jihar Zamfara tun a cikin watan Oktoba aka dawo da na babban jihar wato
Gusau, inda kuma gwamnan ya bada tabbacin cewa a gobe Talata za a dawo da na
sauran kafatanin kananan hukumomin jihar.
A cikin watan Satumban 2021 ne, kimanin wata 3 ke nan, yau ana da adadin kwanaki 89 da
katse sadarwa a kananan hukumomi sha uku (13) na jihar. Hakan ya biyo bayan
zafafa hare-hare da ‘yan bindiga suka rika kai wa a jihar ta Katsina.
Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ne ya bai wa kamfanonin sadarwa a Nijeriya umurnin datse
sadarwar wanda a cewar sanarwar gwamnati, hakan zai bai wa hukumomin tsaro
damar yaki da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane da suka
addabi jihar.
Kananan
hukumomin da aka datse sadarwar sune; Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari,
Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma, Funtua, Bakori, Malumfashi da Kurfi.
Sai
dai wani dan kasuwa mazaunin garin Dandume dake karamar hukumar Dandume, da ya nemi a sakaya sunansa ya
shaidawa wakilinmu cewa yanke sadarwar da aka yi ya tsayar da kasuwancinsu na
sayar da hatsi, wanda ya ce ba shi kadai ba, dukkanin abokan kasuwancinsu sun
jiggata a tsawon wannan lokacin, inda ya yi kira da a dawo musu da sadarwar; “wannan
yanke sadarwar ba ma ni kadai ya shafa ba, ya shafi dukkanin wani alakar
kasuwanci dake babbar kasuwar Dandume ta hatsi musamman da sauran kasuwanni. Kamar
mu da muke kasuwar ‘yan hatsi, muna sayen wa mutane kaya ne daga Kudu, su turo
kudi a saya musu kaya a tura musu, yanke sadarwar nan ya kai ga cewa kasuwa ta
lalace. Ta yadda lokacin da ake tunain a bi kadari, talaka ya samu wani abu,
sai ya zama na ba masu saye gaba daya”, ya tabbatar.
Ya ci
gaba da cewa; “wani lokacin yana zama ba halin waya, sai dai ka tashi ka tafi
har Zariya sannan ka yi waya. Sannan idan ka je Zariya mutanen sun sanya maka
kudinsu, ka taho a hanya kana fargaba saboda za ka iya kai wa yamma, kuma ga
yanayin tsaro na hanya din. Maganar gaskiya yankewa din ya dagula duk lamarin
kasuwanci dake garin Dandume da ma yankinmu gaba daya!”, ya tabbatar.
Shi
kuma wani mazaunin Abuja mai suna Yahaya Muhammad Abdullahi a zantawarsa da
wakilinmu ya koka mana cewa; “yanke sadarwar nan an yi min katangar karfe da
sauraren masoyiyata wanda sauran watanni kadan suka rage mu yi aure. A halin
yanzu ba na jinta, ban san halin da take ciki ba, abubuwan shirye-shirye na
biki sun tsaya saboda ba tattaunawa a tsakaninmu”, ya furta cikin yanayi na
damuwa.
Shin
kwalliya ta biya kudin sabulu?
Wani dan kasuwa mazaunin Dandume, da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yanke sadarwar ba haifar da da mai
ido ba, a cewarsa; “babu wani kwalliya da ta biya kudin sabulu, bai biya ba. Saboda
duk kauyakun da ake tunanin ‘yan bindigar na kai hare-haren, babu inda ba su shiga
ba, sun yi ta’addancinsu ba tare da duniya ta ji me suka aikata ba saboda babu
sadarwa. Ko kwanan nan sun kai wani hari ya ma shafi wadansu abokanmu, an yi
abin sai bayan kwana biyu, aka ji ma labarin abin da ya faru. Ina amfanin yanke
sadarwar? Bai biya ba gaskiya, kawai ana azabtuwa ne!”, ya jaddada.
Sai Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustafa Inuwa, a taron manema labarai da ya kira a
kwanakin baya a lokacin da rahoto ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun fara amfani
da oba-oba wajen sadarwa a tsakaninsu sakamakon yanke sadarwar, ya ce tabbas suna da labarin hakan, kuma tuni jami’an
tsaro suka dukufa tare da masana domin ganin cewa sun hana ’yan ta’addan yin
amfani da wannan na’ura wadda ake zargin wasu bata-gari ne ke samar musu ita ko
kuma ta hanyar saye ta intanet a cewarsa.
Sai
dai a cewarsa yanke sadarwar tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu duk kuwa
da halin kuncin da jama’a suke fuskanta wanda ya ce sai an yi hakuri kafin
ganin an samu nasara a kai.
A cewarsa;
“Kadan daga cikin irin nasarorin da wannan dokar ta samar sun hada da hana
samun bayanai daga masu ba su labari a kan inda za su kawo hari ko shigar
jami’an tsaro domin kai musu farmaki.
“Yin
garkuwa da mutane ya yi sauki fiye da baya; dokar ta rage yawan kwacen babura
da kuma shigar musu da man fetur da suke amfani da shi suna zubawa ababen
hawansu.”
Sakataren
gwamnatin ya kara da cewa, idan aka lura daga lokacin kafa dokar zuwa yau,
misali a tsakanin watan Yuli da Agusta na 2021 an samu rahotannin yin garkuwa
da mutane har 173 wanda ya shafi mutane 475.
Amma
a tsakanin watan Satumba da Oktobar 2021 an samu rahoton garkuwa da mutanen sau
61 wanda ya shafi mutane 102 kamar yadda Aminiya ta labarto.
Me masana
ke cewa kan datse sadarwar?
Su kuma
masana a Nijeriya na bayyana damuwa kan matakin da gwamnatin Nijeriya ta ɗauka
na toshe hanyoyin sadarwar.
Malam Kabiru Adamu, wani masanin harkokin tsaro na ganin cewa an sha ɗaukar irin waɗannan
matakan amma ba tare kawo ƙarshen matsalar tsaron ba. Kuma toshe layukan
sadarwar zai yi matukar tasiri ga jefa mutanen yankin cikin mawuyacin hali.
Haka
kuma masanin ya ce ƴan bindigar za su iya amfani da hanyoyin sadarwa na
tauraron ɗan adam da kuma intanet. Don haka suna da zaɓi na hanyoyin da za su
yi amfani da su domin sadarwa, a cewarsa.
Sannan
matakan a cewar masanin za su shafi tattalin arziki da jefa jama'a cikin
wahala.
-Rahoton MADOGARA
No comments