Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Haramta 'Yan sa-kai An Halasta 'Yan Banga A Jihar Sakkwato

Gwamnatin Sakkwato ta haramta ayyukan ƴan sa-kai a faɗin jihar tare da ƙarfafa aikin ƴan banga. Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Ta...


Gwamnatin Sakkwato ta haramta ayyukan ƴan sa-kai a faɗin jihar tare da ƙarfafa aikin ƴan banga.

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ne ya sanar da ɗaukar matakin a ranar Litinin a wani taron tsaro na jihar, ya ce sha’anin yan sa-kai shi ya ƙara haifar da matsala a Zamfara da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Majiyarmu ta BBC ta labarto gwamnan na cewa; suna yin gaban kansu ba tare da bin doka da oda ba. “Ba za mu ci gaba da kyalewa ba domin mun san illar hakan.”

“Mun fito da doka da ta haramta ƴan sa-kai kuma duk wanda ke son taimakawa jami’an tsaro, to ya shiga aikin banga,” in ji gwamna Tambuwal.

Sanarwar da ofishin gwamnan ta fitar ta ce duk wanda aka kama zai sha ɗaurin shekara 14 ko biyan tara ta naira 500,000.

Dokar ta kuma ce duk wanda aka kama da makami a jihar zai sha ɗaurin shekara bakwai a gidan yari ko ya biya tarar naira 200,000.

Gwamna Tambuwal ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin ne domin magance matsalolin tsaro da ke damun jihar.

Kuma matakan hanyoyi ne na inganta sha’anin aikin ƴan banga domin taimakawa jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

No comments