BBC ta labarto cewa; Hukumar ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Nijeriya ta ce an samu ƙarin mutum 110 da suka kamu da cutar korona a N...
BBC ta labarto cewa; Hukumar ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Nijeriya ta ce an samu ƙarin mutum 110 da suka kamu da cutar korona a Nijeriya.
Alƙalumman sun nuna mutum 27 suka kamu da cutar a jihar Imo sai a jihar Katsina da aka samu mutum 23 a ranar Lahadi.
A jihar Rivers an samu mutum 20, sai jihar Ondo mai mutum 11. A Kaduna ƙarin mutum tara suka kamu da cutar.
Yanzu jimillar mutum 214,092 cutar ta shafa a Najeriya amma 207,254 sun warke yayin da cutar ta kashe mutum 2,976 a Nijeriya.
Ga jihohin da aka samu ƙarin cutar a Najeriya a ranar Lahadi.
Imo-27
Katsina-23
Rivers-20
Ondo-11
Kaduna-9
FCT-6
Oyo-6
Plateau-3
Osun-2
Ekiti-1
Gombe-1
Zamfara-1
No comments