Amurka ta gargadi China kan zancen da ta kirkira ta jinginawa Rasha game da yunkurin da ta ce Chana na yi na taimakawa Rasha a yakin da ta...
Amurka ta gargadi China kan zancen da ta kirkira ta
jinginawa Rasha game da yunkurin da ta ce Chana na yi na taimakawa Rasha a
yakin da take yi da Ukraine, inda ta ce matukar China ta taimakawa Rasha to
tabbas za ta dandana kudarta.
Bayanai dai daga Amurka na cewa ta karkashin kasa
Rasha ta nemi tallafin Ukraine na karin sojoji da kayayyakin yaki, kuma China
na duba yiwuwar taimaka mata, abin da a cewar Amurka zai kara tsananta yakin.
Sai dai kuma tuni ma’aikatar harkokin wajen China ta
musanta zargin, inda ta ke cewa da gangan Amurka ta bullo da wannan zancen don
kawai jefa ta cikin rikicin da gangan.
Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawa ta musamman
da aka yi a tsakanin ministocin kasashen wajen Amurka da China a birnin Rome.
A yanzu haka dai bayanai na cewa za a koma ci gaba
da tattaunawar zaman lafiya a tsakanin kasashen Ukraine da Rasha karo na Hudu a
gobe Talata.
A cewar guda daga cikin tawagar Ukraine a tattaunawa
da Rasha, Mikhailo Podolyak ta cikin wata wallafar shafin Twitter, ya ce yana
fatan a wannan karo za a cimma matsaya.
No comments