Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zanga-zanga Ta Barke A Faransa Bisa Azabtar Da Dan Gwagwarmaya

  Wata mummunar zanga-zanga ta barke a garin Corsica na Faransa sakamakon cin zarafin Dan gwagwarmayar kwato hakkin dan adam din nan dake ts...

 


Wata mummunar zanga-zanga ta barke a garin Corsica na Faransa sakamakon cin zarafin Dan gwagwarmayar kwato hakkin dan adam din nan dake tsare a gidan yari tun shekarar 2003 wato Yvan Colonna.

Al’ummar garin na wannan zanga-zanga ne don nuna fushin su game da cin zarafin dan gwagwarmayar kwato hakkin Dan adam Yvan Colonna da ke tsare a gidan yari tun shekarar 2003.

Tun farko dai an yanke masa hukuncin daurin rai da rai ne sakamakon kama shi da hannu a kisan magajin garin wato Corsica, Calude Erignac, bayan lakada masa duka, abin da ya yi sanadiyyar shigarsa dogon suma kafin daga bisani ya mutu a ranar 2 ga watan Maris din 1998 a cewar rahoton mahukumta.

Yvan wanda ke tsare a wani gidan yari dake Kamaru kuma jama’ar garin na samun labarin cewa yana fuskantar muzgunawa da kuma cin zarafi a gidan yarin, abin da ya tashi zanga-zangar.

Tun farko dai a cewar kafafen yada labaran cikin gida jama’a sun fusata ne bayan samun rahoton Mutuwar Yvan saboda karancin Iska wadda aka hana shi da gangan a gidan yarin, sai dai kuma daga baya hukumomin gidan yarin sun musanta batun mutuwar tasa.


No comments