Kungiyar Malaman jami’o’i ta Nijeriya wato ASUU ta tsawaita yajin aikin gargadi da take yi da makwanni takwas. Inda ta bayyana dalilanta...
Kungiyar Malaman jami’o’i ta Nijeriya wato ASUU ta
tsawaita yajin aikin gargadi da take yi da makwanni takwas. Inda ta bayyana
dalilanta na yin hakan.
An dai cimma wannan matsaya ne bayan taron majalisar
zartarwa kungiyar malaman jami’o’in na kasa da safiyar ranar Litinin a
hedikwatarta da ke Jami’ar birnin Abuja.
Jim kadan bayan taron ne shugaban kungiyar ta ASUU
Emmanuel Osodeke ya ce karin wa’adin ya fara aiki ne daga karfe 12:01 na safe
na ranar Litinin 14 ga Maris, na shekara ta 2022.
Sanarwar ta bayyana takaicin yadda gwamnati ta ki
mayar da hankali wajen kula da bukatun da suka gabatar mata a tsawon tsawon
makwanni hudu da suka shafe suna yajin aikin gargadi.
A ranar 14 ga watan Fabarairun da ya gabata ne dai
kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya ASUU, ta shiga yajin aikin gargadi na wata
daya, domin neman gwamnati ta cika alkawarin mutunta yarjejeniyoyin da suka
cimma, wadanda suka ba da damar dakatar da dogon yajin aikin da suka yi a
shekarar 2020.
No comments