Magoya bayan Paris Saint-Germain a gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, sun yi wa fitattun ‘yan wasan kungiyar da suka hada da Lionel Messi da ...
Magoya bayan Paris Saint-Germain
a gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, sun yi wa fitattun ‘yan wasan kungiyar da
suka hada da Lionel Messi da Neymar ihu a ranar Lahadi, yayin buga wasansu na
farko tun bayan da Real Madrid ta fitar dasu daga gasar cin kofin zakarun Turai
a ranar Laraba.
PSG da ke jagorantar
gasar ta Ligue 1 sun fafata ne da Bordeaux, inda kuma magoya bayan ta suka rika
yi wa 'yan wasan kungiyar ihun adawa da kuma fito a duk lokacin da suka taba
kwallo, musamman ma Messi da Neymar.
Sai dai Kylian Mbappe,
wanda mai yiwuwa ya koma Real Madrid nan gaba kadan, bai fuskanci bacin ran
masu kallon ba, kasancewar ya taka rawar gani wajen cin kwallaye a dukkanin
karawar da suka yi da jagororin na gasar La Liga ta Spain.
Daga karshe dai kungiyar
PSG ta samu nasara kan Bordeaux da kwallaye 3-0, wadanda Mbappe da Neymar da
Paredes suka jefa.
A halin yanzu kungiyar
ke kan gaba a gasar Ligue 1 da maki 65, tazarar maki 15 a tsakaninta da
Marseille, waddake matsayi na 2.
No comments