Rfi ta labarto cewa; babban Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce kungiyar ba za ta kakaba dokar hana zirga-zirgar jir...
Rfi ta labarto cewa; babban Sakataren kungiyar tsaro
ta NATO Jens Stoltenberg ya ce kungiyar ba
za ta kakaba dokar hana zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Ukraine
ba, biyo bayan kiraye kirayen da mahukuntar kasar ke yi na taimakawa wajen taka
wa Rasha birki a kan luguden wuta da take yi a kan kasar.
A yayin wani
taron gaggawa na ministocin harkokin waje na kasashen NATO, Stoltenberg
ya ce hanya daya tilo da za a bi wajen aiwatar da dokar hana zirga zirgar
jiragen sama a Ukraine ita ce ta harbo jiragen saman Rasha, kuma yin haka zai
kai ga babban yaki a Turai, wanda zai shafi kasashe da dama.
Stoltenberg ya yi kashedin cewa al’amura na iya
rincabewa fiye da yadda ake gani a yanzu a
kwanaki masu zuwa, inda za a samu karin asarar rai da wahalhalu da
barnace barnace, duba da yadda Rasha ke shigowa da manyan makamai tare da ci gaba
da hare hare a fadin kasar.
NATO, wadda ta ce wannan yaki ba nata bane, ta dau
wannan mataki ne duk da magiyar da
shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke yi ta a taimaka masa wajen
dakatar da luguden wutar da Rasha ke yi a biranen kasarsa.
Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya
gabatar da jawabi ga taron ta kafar bidiyo, inda ya mika bukatar daukar mataki
kafin a makara, yana mai cewa a shirye suke su kare kansu, amma suna neman
taimako.
No comments