Dakarun Rasha sun kai hari kan tashar nukiliya mafi girma a Turai da safiyar yau Jumma’a, matakin da ya haifar da gobara a cibiyar dake ts...
Dakarun
Rasha sun kai hari kan tashar nukiliya mafi girma a Turai da safiyar yau
Jumma’a, matakin da ya haifar da gobara a cibiyar dake tsakaiyar Ukraine, inda shugaban kasar ya zargi Moscow
da "ta'addancin nukiliya".
Harin
ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Rasha suka kara kaimi wajen kai hare-hare
a garuruwa da dama a kasar ta Ukraine da suka hada da Chernihiv da ke arewacin
kasar, inda jami'ai suka ce fararen hula 33 ne suka mutu.
Tuni
shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Moscow da "ta'addancin
nukiliya" jim kadan bayan da sojojin Rasha suka kai hari cibiyar samar da
wutar lantarki ta Zaporizhzhia, tashar nukiliya mafi girma a Turai, dake
gabashin birnin Energodar.
Hukumomin
yankin suka ce harin baiyi barna sosai ba, kuma gobarar ba ta shafi “mahimman”
kayayyakin cibiyar Nukiliyar ba, ko da yake har yanzu ba a san abin da zai biyo
baya ba.
Hukumar
bada agajin gaggawa a yankin Chernihiv da ke gabashin kasar ta ce an ciro
gawarwaki mutane 33 daga baraguzai bayan ruwan bama-bamai da dakarun Rasha suka
kai ta sama, wanda gwamna Viacheslav Chaus ya ce harin ya shafi gidaje da
makarantu biyu.
Yayin
da take ci gaba da luguden wuta a bangare daya, Kasashen na Rasha da Ukraine
sun amince da bukatar samar da hanyoyin jin kai domin kwashe fararen hula, tare
da yiwuwar tsagaita wuta, kamar yadda babban mai shiga tsakani na Rasha
Vladimir Medinsky ya bayyana bayan tattaunawa da Ukraine.
No comments