Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yakin Ukraine Ka Iya Haddasa Yunwa A Kasashen Larabawa

  Shugaban Algeria AbdelMajid Tebbourne ya haramta fitar da kayayyakin abinci zuwa kasashen ketare a daidai lokacin da ake ci gaba da fargab...

 


Shugaban Algeria AbdelMajid Tebbourne ya haramta fitar da kayayyakin abinci zuwa kasashen ketare a daidai lokacin da ake ci gaba da fargabar tashin farashin kayayyakin abinci saboda rikicin Rasha da Ukraine, yayin da masana ke cewa, matsalar ka iya haifar da yunwa a kasashen Larabawa.

Kayayyakin abincin da Algeria ta haramta fitar da su sun hada da Sikari da Man-gyada da Taliya da Garin Masara na Semolina da kuma sauran nau’ukan abincin da ake samar da su daga alkama.

Shugaban na Algeria ya dauki matakin ne bayan ya saurari jawabin da Ma’aikatun Noma da Kwadago na kasar  suka gabatar masa game da abincin da aka fi ta’ammulli da su a kasar.

A bangare guda, rahotanni na cewa, iyalai da dama a daukacin sassan  yankin Arewacin Afrika na ci gaba da rige-rigen sayo nau’ukan abinci irinsu filawa da garin masara suna adana su, saboda fargabar tashin farashin abinci a dalilin yakin  Rasha da Ukraine.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage ‘yan makwanni a fara gudanar da azumin watan Ramnadan, lokacin da iyalai suka fi wadata kansu da abinci.

Tunisia da Morocco da Libya da sauran kasashen Larabawa, na shigo da alkama ne daga Rasha da Ukraine da ke gwabza yaki a yanzu haka, abin da ya sa ake ganin cewa, babu shakka wannan tashin hankalin zai jefa yankin na Arewacin Afrika cikin wani mummunan yanayi na karancin abinci.

Wasu ma na fargabar cewa, yakin na Rasha da Ukraine zai haddasa yunwa da kuma tarzoma a kasashen Larabawa, kamar dai yadda aka taba gani shekaru 10 da suka wuce.


No comments