Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwame Nkrumah Ɗan Gwagwarmayar Kwatar 'Yanci Ya Cika Shekaru 50 Da Rasuwa

Yau ake cika shekaru 50 da rasuwar shugaban Ghana na farko Dakta Kwame Nkrumah, wanda aka yi wa juyin mulki a shekarar 1966. Al’...



Yau ake cika shekaru 50 da rasuwar shugaban Ghana na farko Dakta Kwame Nkrumah, wanda aka yi wa juyin mulki a shekarar 1966.

Al’ummar Ghana da ma nahiyar Afirka na tunawa da gwarzon shugaban saboda rawar da ya taka wajen neman ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka da kuma manufofinsa na neman ci gaban bakar fata.

Nkrumah ya rasu ne a ranar 27 ga Afrilu na shekarar 1972 yana da shekaru 62, yayin da yake fama da cutar daji, inda ya rasu a Bucharest babban birnin kasar Romania.

An hambarar da gwamnatin Dakta Kwame Nkrumah ne a wani juyin mulki da Kanar Emmanuel Kwasi Kotoka ya jagoranta a ranar 24 ga Fabrairu, na shekarar 1966, a lokacin da shugaban ke gudanar da ziyarar aiki a kasar waje.

No comments