Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta cire minista mata da jinkai, Mrs. Uju Kennedy- Ohenenye daga kan m...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta cire minista mata da jinkai, Mrs. Uju Kennedy- Ohenenye daga kan matsayin ta domin rashin sanin makaman aiki da shiga hurumin da bai shafi aikin ta ba. Majalisar limaman juma'a a jihar Neja ne tayi kiran bayan wani zaman gaggawa da majalisar tayi yammacin jiya laraba kan kudurin minista na aurar da yara marayu da suka rasa iyayen su sakamakon hare haren yan bindiga a yankin su.
Majalisar ta baiwa minista kwanaki bakwai da ta janye kalaman ta na batanci da tunzurin haddasa fitina a cikin al'umma. Matakin ministan na neman shugaban rundunar yan sanda ta kasa da zuwa kuto dan ganin an dakatar da aurar da yara mata marayu dari da majalisar limaman tayi kutse akan hurumin da bai shafi ministan ba, domin abinda limaman suka shirya na aurar da yaran bai sabawa dokokin kasa da addinin musulunci ba, saboda dukkanin yaran da aka tantance sun kai shekarun aure.
Sakataren limaman juma'a a jihar Neja, Sheikh Umar Faruq Abdullahi ( Sarkin Malaman Nupe) shi ya yiwa manema labarai karin haske bayan zaman majalisar.
Ya cigaba da cewar bukin auren ba shugaban majalisar dokokin, Rt. Hon. Abdulmalik Sarkin-daji ya shirya shi ba, majalisar limaman ne ta shirya shi, illa shi an nemi gudunmawarsa ne akan hidimar auren, kuma ya bada saboda kamar yadda majalisar ta shirya bukin ranar 24 ga watan Mayun shekarar nan yana nan daram ba fashi.
Tun farko mun kafa kwamitin tantancewa kuma mun bada sharudda guda shida, idan yarinya ta kasa cika sharadi guda ba za ta shiga cikin shirin ba, maganar karancin shekaru ba gaskiya ba ne domin yaran shekarun su na haihuwa daga sha takwas ne zuwa ashirin da biyar, dan haka matakin Mrs. Uju Kennedy mataki ne na kutsewa addinin musulunci da yunkurin kawo fitina a cikin al'umma.
Dan haka muna shawartar gwamnatin tarayya da ta gaggauta cire ta a matsayin ministan jinkan mata kuma ta haramta mata rike kowani irin mukami domin ba ta san aikinta, kuma ta jahilci yadda ake shugabantar al'umma.
Bayan nan mun baiwa Mrs. Uju Kennedy kwanaki bakwai da ta janye kalamanta in ba haka ba za mu dukufa gaban shari'a da ita, dukkanin shirye shiryen auren mun yi shi ne da masana dokokin kasa, saboda dukkanin bayanan mu mun gabatar da su ga lauyoyin mu kuma ba abinda zai hana wannan auren a ranar da muka shirya shi.
Maganar dakatawar kotu, wannan abu ne da ya shafi shugaban majalisar da ita ministan da ke masa zagon kasa domin bai shafi abinda muka sanya gaba na auren marayun ba.
Dan haka muna kira ga masu hannu da shuni da yan siyasa da su fito da abinda ke hannun su wajen tallafawa mabukata da marayu wajen share masu hawaye ta hanyar tallafawa rayuwarsu musamman akan ayyukan alheri kamar yadda maigirma shugaban majalisar dokokin jihar Neja ke yi idan bukatar hakan ta taso.
Yana bada tallafin ilimi, taimakawa mabukata, da sauran jinkai ga marasa galihu.
Tun zuwan Mrs. Uju Kennedy ba mu taba jin wani gudunmawar da ta baiwa yara marayu da suka rasa iyayen su sakamakon hare haren yan bindiga da wadanda suka rasa iyaye sanadiyar rikicin boko haram ba, ta hanyar daukar dawainiyar ilmantar da su ko ba su agajin gaggawa dan rayuwarsu ta inganta ba
Saboda haka mu limaman masallatan juma'a a jihar Neja da suka shafi limaman masallatan JIBWIS Kaduna da Jos, da limaman masallatan sufaye mun yi tis da Allah waddai da wannan irin salon jagorancin Mrs. Uju kan kutse da batanci ga shugaban majalisar dokokin Neja da addinin musulunci kuma ba za mu lamunci hakan ya cigaba da faruwa a kasar nan ba.
No comments