Gwamnatin Karamar Hukumar Suleja ta jihar Neja ta rufe kasuwar Madalla dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Da yake zantawa da manema labarai...
Gwamnatin Karamar Hukumar Suleja ta jihar Neja ta rufe kasuwar Madalla dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Karamar Hukumar Isyaku Bawa Na'ibi, yace daukar matakin ya biyo bayan tuburewa da Yan kasuwan keyi na cin kasuwa akan titi.
Na'ibi ya ce ba zai yuwwu su lamunci shiga hakkokin Al'umma da suke yi ba.
Kasuwar wacce take ci a duk ranar alhamis na zama barazana ga Matafiya a duk yammacin laraba da kuma alhamis.
Bayan rantsar da Gwamna Umaru Mohammed Bago kasuwar ce ta farko da ya fara kai ziyara, inda ya bukaci su matsa daga bakin titi bayan kwana biyu kuma suka koma gidan jiya.
Wannan ne dalilin da yasa shugaban Karamar Hukumar ya dauki matakin rufe kasuwar har illa Masha Allahu.
No comments