Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisan Ɗinkin Duniya Ta Yaba Da Harkar Haƙar Ma'adanai Da Gwamnatin Nasarawa Ke Bunƙasawa

Daga Zubairu Lawal Lafia Da take jawabi a taron bunqasa harkokin masu zuba jali da bunqasa harkan masana'antu da Gwamnatin j...

Daga Zubairu Lawal Lafia

Da take jawabi a taron bunqasa harkokin masu zuba jali da bunqasa harkan masana'antu da Gwamnatin jihar Nasarawa ta shirya karo na biyu.

Babban mataimakiyar Sakatariyar Majalisan Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad tace; Majalisan Dinkin Duniya ta baiwa jihar Nasarawa dama wajen gudanar da bunqasa harkan haqar Ma'adanai saboda bunqasa harkan tattain arziki a jihar  da kasa baki daya.

Babban mataimakiyar Sakatariyar Majalisan Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad Wanda ta samu halartan taron  ta Na'urar Majigi ta hoto mai motsi tace; tayi farin ciki da Gwamnatin jihar Nasarawa ta sanyan Samar da masu zuba jali da bunqasa albarkatun kasa dake fadin jihar.

Tace; hakiqa al'umman jihar Nasarawa zasu amfana da kuddurin Gwamnatin wajen janyo masu zuba jali da bunqasa harkan Noma a jihar.

Shima a nasa jawabin Shugaban Kasar Nijariya Bola Ahmad Tinubu ya yabawa kuddurin Gwamnatin jihar Nasarawa wajen janyo yan Kasashen waje dake zuba jali a jihar.

     Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yace gwamnatinsa zata cigaba da taimakawa gwamnatocin jihohi Qasarnan domin habakar kowane Bangarorin musamman sha'anin ma'adanai da harkan aikin noma.

     Shugaban Kasan Bula Ahma Tinunu Wanda Karamar Ministan harkokin zuba jali da bunqasa harkan haqar Ma'adanai Misis. Doris Uzoka Anite, ta wakilta yace; Allah ya albarkaci Nijariya da dumbin albarkatun qasa ya zama dole mu jajirce wajen haqar Ma'adanai domin bunqasa harkan tattalin arziki da zai amfani al'umma.

Tace; jihar Nasarawa tana da gandon daji da wadatattun filayen gona Wanda al'umma ke amfana. Ta kuma yabawa Gwamnatin jihar da ta Samar da hadin giwa da kamafanin Factory at Kama Otto dake Karamar hukumar  Nasarawa.

Tun farko a nasa jawabin  Gwamna Abdullahi Sule yayi godiya ga manyan baqi da suka halarci wannan taron karo na biyu a jihar.

Yace; tun farkon darewasa kujerar Gwamnan masu zuba jali suka riqa tururuwa suna buqatar zuba jali da bunqasa harkan haqar Ma'adanai a jihar.

Gwamnan yace; bazasuyi qasa a giwa ba wajen qara janyo masu zuba jali daga ko ina domin cigaban jihar Nasarawa.

Shima Shugaban harkan zuba jali ta jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Abdullahi NASIDA. Yace; ofishinsa ta samu gagarumin cigaba wajan Samar da masu zuba jali a jihar Nasarawa.

No comments