Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CEDDERT Ta Shiryawa Dakatai Taron Ƙarawa Juna Sani Kan Matsalar Tsaro A Zazzau

Daga Idris Umar, Zaria Wata cibiya mai zaman kanta wato cibiyar samar da horo da bincike da cigaban damakaradiyya (CEDDERT) za t...


Daga Idris Umar, Zaria

Wata cibiya mai zaman kanta wato cibiyar samar da horo da bincike da cigaban damakaradiyya (CEDDERT) za ta haɗu da masarautun gargajiya domin nuna masu muhimmancin bukatar da ake da ita na al'ummu su shiga cikin samar da tsaro a fadin masarautar Zazzau, kamar yadda babban daraktan cibiyar, Farfesa Abubakar Sadik ya bayyana yayin taron nunawa sarakunan gargajiyar muhimmancin a masarautar Zazzau wanda aka yi a Zariya.

Farfesa Abubakar Sadik a cikin wata kasida da ya gabatar mai taken "rawa da nauyin da ya hau kan masu sarautun gargajiya kiran a farka", ya nuna cewa masu sarautun gargajiya ya kamata a basu rawar da za su taka a tsarin mulki domin ya kasance sun bayar da tasu gudummuwar wajen tsaron al'ummunsu.

Ya yi kira ga mahalartan da su yada ilimin da suka samu ga wadanda suke mulka domin daina shigar da matasa cikin harkokin fashi sakamakon abin da ka iya biyo baya da kuma kudade wadanda ba na halas ba.

Bayan haka, yayin da ya ke gabatar da tasa ƙasidar, daya daga cikin daraktocin cibiyar, Farfesa Mustafa Umar Gwadabe, ya bayyana cewa cibiyar ta gudanar da bincike a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, Zamfara da Katsina wanda ya nuna cewa matasa sun shiga cikin yin garkuwa da mutane da ayyukan fashi ne ta hanyar janyo hankalinsu da kudi da kuma ƙwayoyi.

A cikin jawabinsa, shugaban taron, Wazirin Zazzau Alhaji Muhammad Inuwa Aminu ya yi kira ga Dakattai da sarakunan kauyuka da su gudanar da irin tarukan a yankunansu domin samun biyan buƙata.

Yayin da ya ke bayani a kan al'amarin fashi da garkuwa da mutane a yankinsa, Kaigaman Zazzau Dakacin Kidandan, Alhaji Nuhu Umar ya ce a cikin kimanin sama da shekaru bakwai kashi casa'in na yaran makaranta sun bar makaranta saboda dakatar da malamai da gwamnatin Nasiru El-rufai ta yi kuma waɗanda aka canzawa wuraren aiki ba su zuwa ayyukan saboda rashin tsaro.

Kaigaman ya ce dubunnan hektocin gona ba za a iya nomasu ba saboda ba mai so ya je gonarsa kuma al'ummu da dama sun bar gidajensu domin rashin tsaro.

Taron ya samu halartar jami'an tsaron hukumar hana sha da tu'ammali da miyagun kwayoyi (NDLEA) kuma hukumar jami'an tsaron farin kayan Nijeriya (NSDS) ta gabatar da ƙasida a yayin  taron.

No comments