Daga Hussaini Yero, Funtua Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda, ya jaddada bukatar gwamnati ta kara tsaurara matakan tsaro...
Daga Hussaini Yero, Funtua
Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda, ya jaddada bukatar gwamnati ta kara tsaurara matakan tsaro da kyakkyawar kulawa akan iyakokin kasarnan inda ya ce ta nan ne ake shigowa da makamai da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa, wanda ya dabaibaye shugabani da amanar al'umma ke hannun mu,idan aka magance wadannan abu zai taimaka matuka wajen magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da lacca ta biyu na bikin amsar sabin dalibai A Jami’ar Tarayya da ke Gusau, A Yau Juma'a.
Gwamna Rada,Ya bayyana jahilci,Cin Rashawa ga shugabanni da shugabanci, rashin yarda da addini da shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo tabarbarewar tsaro da ke kawo illa ga ci gaban ilimi akowace nahiya.
Gwamna Radda ya ce, yawaitar satar yara ‘yan makaranta da 'yan gudun hijira na haifar da rashin zuwa makaranta, wanda anan gaba zai zama illa ga Kasar nan.
Akan haka ne Gwamna Rada yayi kira ga Shugabanni da suji tsoran Allah akan amanar da suka dauka na kare alumma da ilmantar da su.da kuma ba tsami'an tsaron mu Kyakkywar kulawa musamman masu kula da Boda watau iyakokin shigowa kasar nan.yin haka shine zai taimaka wajan dakile matsalar tsaron da ta'addabe mu .inji gwamna Diko Radda.
No comments