Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sultan Sa'adu Ya Buɗe Makarantar Tsangaya Ta Kwana Da Asibiti A Zamfara

Daga Hussaini Yero, Gusau Mai martaba, Sarkin Musulmi, Sa'adu Abubakar Na 3 ya jagorancin bude Makarantar Tsagaya ta Kwana a...


Daga Hussaini Yero, Gusau

Mai martaba, Sarkin Musulmi, Sa'adu Abubakar Na 3 ya jagorancin bude Makarantar Tsagaya ta Kwana a Karamar Hukumar Gumi da Asibiti A Nasarawan Bulkulu da ke cikin karamar hukumar Bukuyum a Jihar Zamfara.

A jawabin sa ,Sultan Sa'adu Abubakar ya bayyana Jindadin sa ganin yadda gwamnatin Jihr Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal wajan Bunkasa Ilimin addini da na Zamani."

"Wannan Makaranta zata taimaka gaya wajan samun ingantacen Ilimi addini da na Zamani,akan haka ne Sultan Sa'adu Abubakar yayi kira ga gwamnoni da suyi koyi da irin wannan shirin gwamna Dauda na Bunkasa Ilimin na addini da na Zamani.kuma yayi kira ga alumma da zasu amfana da wannan tsanga su kasance masu aiki tukuru tsakani da Allah da kuma rike amar da aka basu inji Sultan Sa'adu Abubakar.

Anasa jawabin gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa,tun lokacin yakin nemam zabe mukayi ma al'uma alkawari samar masu Ilimi,wanda yanzu haka mun dukufa wajan gyara Makarantun da Gina sabi a fadin Jihar.inji gwamna Dauda."

"Gwamna Dauda Lawal ya kuma tabbatar da cewa zasu dauki nauyin Makarantar da kula da ita . kuma wannan Tsangaya guda uku ce mukayi a cikin wannan,akwai a Gusau da Kauran Namoda.

Gwamna Dauda ya kuma sanya ma Makarantar Tsagayar Gumi suna Sultan Abubakar Sa'adu Na 3.shine sunan Tsagayar da za'a rinka kiran ta inji gwamna Dauda Lawal.

No comments