Daga Awwal Umar Kontagora An nemi al'umma da su jajirce wajen hadin kai da yin addu'o'i musamman ganin halin da kasar nan ke cik...
Daga Awwal Umar Kontagora
An nemi al'umma da su jajirce wajen hadin kai da yin addu'o'i musamman ganin halin da kasar nan ke ciki tana bukatar komawa ga Allah. Shugaban kungiyar mahaddata Alqur'ani mai tsarki da malaman tsangaya ta kasa reshen arewa ta tsakiya, Amb. Gwani Musa Adamu yayi kiran a lokacin zantawarsa da manema labarai a Minna.
Ambasadan ya cigaba da cewar jihar Neja tayi nasarar samun gwamna mai kishi wanda yake da jihar a zuciyarsa, dole wadanda ke zagaye da shi su marasa masa baya kan wannan kudurin, sannan talakawa su ba shi goyon baya.
Lokacin da gwamnatin tazo mun sha alwashin cigaba da yin addu'o'in zaman lafiya lokaci zuwa lokaci sakamakon halin rashin tsaro da muke ciki, wanda gwamnati ta sha alwashin daukar nauyi a kowani karshen wata. Daga baya wasu mashawarta wadanda ba sa son cigaba suka kanididiye saboda dan abinda suke samu sakamakon rashin zaman lafiya a jiha, haka abin yake har a sama, to daman Allah ya fadi irin wadannan mutanen a cikin Alqur'ani mai tsalki.
Babu abinda suke fadi tashin samu sai dan wani abu, wanda ba komai suke ci daga cikinsa ba face wuta. Saboda maganar yiwa jiha da kasa addu'o'in zaman lafiya kungiyar Huffazu ba za janye ba, muna kara kira ga malaman tsangayu da su kara kaimi wajen yin addu'o'in nan domin idan kasa ta samu zaman lafiya kowa zai anfana.
Shugaban ya bayyana cewar mun yaba kuma mun gamsu da matakan da gwamnati ke dauka wajen lalubo hanyoyin daidaita abubuwa, amma muna kara jan hankalin gwamnati dan gane da shirinta na sauya fasalin makarantun tsangayu da ta tabbatar tayi aiki ka'in da na'in wajen ganin am kafa ginshiki mai inganci da zai zamo alheri ga jihar nan game da makarantun tsangayu.
Idan gwamnati ta ba mu dama muna da tsare tsaren da idan muka gabatar ma ta kakkabewa kawai za ta yi, ayi gyaran fuskar da zai zama mai anfani.
Amb. Musa, ta jawo hankalin sauran yan siyasa da su yi koyi da salon jagorancin manomi gwamna Umar Bago wajen samar da abubuwan cigaba ga jama'ar su, yanzu haka hanyoyi kawai gwamna ya tabbatar zai guda dari biyar da ashirin da shida ne a jihar nan.
Yanzu an samu damar kammala wannan aikin cikin shekaru biyu, Neja za ta zama jihar da ta fi kowace jiha dacen cin moriyar mulkin dimukuradiyya.
Shugaban tayi kira ga sauran shugabannin kungiyoyi musamman na addini da su zama jagororin hadin kai ga jama'a da cire bambancen bambancen da ke tsakanin su dan cigaba da samun zaman lafiya tsakanin al'ummar jiha. Maganar gaskiya wasu malaman su dauki hanyar rarraba kawunan jama'a a matsayin hanyar cin abincin su wanda wannan kuskure ne babba.
No comments