Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Sake Duba Ƙarin Kuɗin Lantarki - Gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake duba maganar ƙarin kuɗin lantarki da aka yi wa 'yan ajin Band A a watan da ya gabata sakamakon zanga...


Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake duba maganar ƙarin kuɗin lantarki da aka yi wa 'yan ajin Band A a watan da ya gabata sakamakon zanga-zangar da 'yan ƙungiyar ƙwadago suka gudanar a yau Litinin.

Da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi a Abuja, babban sakatare a ma'aikatar lantarki Mamudah Mamman ya faɗa wa 'yan ƙwadagon cewa tuni majalisar ƙasa ta nemi gwamnati ta ƙara neman shawarar masu ruwa da tsaki kan ƙarin.

A safiyar yau ne mambobin ƙungiyar ta NLC suka yi wa ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki tsinke a faɗin ƙasar, ciki har da Aedc na Abuja.

"Abin da za mu yi shi ne komawa kan teburi, mu sake kallon abin, kuma mu ƙarƙare abin da ya fi dacewa. Ba ni da ikon janye ƙarin amma za mu koma fagen tattaunawa da hukumomi da kuma NLC," in ji shi kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa zan ɗauki saƙonku zuwa hukumomin da suka dace, kuma za mu duba mu kawo muku rahoto".

A watan Afrilu ne hukumar Narc ta amince da ƙarin N225 kan kowane kwh ɗaya daga N66, kafin daga baya a rage shi zuwa N206.80.

No comments