Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji sun kashe 'jagoran 'yanfashi Dogo Bangaje' a Kaduna

Ma'aikatar tsaro ta gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce jami'an tsaro sun kashe wani jagoran 'yanfashin daji ma...


Ma'aikatar tsaro ta gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce jami'an tsaro sun kashe wani jagoran 'yanfashin daji mai suna Dogo Bangaje tare da abokan aikinsa uku.

Wata sanarwa da Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Punch ne suka yi nasarar kashe 'yanbindigar a ƙaramar hukumar Giwa.

"Dakarun sun fara kai samame ƙauyen Tumburku da kuma Sabon Sara, inda suka kashe mutum biyu tare da ƙwace abubuwa da suka haɗa da babura, da wayar hannu, da sigari, da layoyi, da jakunkunan leda cike da man fetur," in ji kwamashinan.

"An kai irin wannan hari a ƙauyen Basurfe, inda dakaru suka murƙushe 'yanfashin dajin da suka yi musu ƙofar rago kuma suka kashe biyu daga cikinsu. Daga baya kuma suka gano wani sansaninsu a cikin daji.

"Daga cikin abubuwan da aka ƙwato akwai bindigar AK-47, da harba-ruga, da jakar harsasai 16, da rediyo biyu, da bam, da babur, da wayar hannu, da ƙwayoyi, da sigari, da sauran kayan kiwon lafiya."

Aƙalla mutum 1,097 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilun da ya gabata - akasarinsu sakamakon hare-haren 'yanbindiga - a cewar wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting ya fitar a yau Litinin.

No comments