Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NFF ta gabatar da Finidi George a matsayin kocin Nijeriya

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta ƙaddamar da Finidi George a hukumance a matsayin kocin tawagar ƙasar ta Super Eagles na dindindin ba...



Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta ƙaddamar da Finidi George a hukumance a matsayin kocin tawagar ƙasar ta Super Eagles na dindindin bayan sanar da sunansa a ƙarshen watan da ya gabata.

Tsohon ɗan wasan na tawagar Super Eagles, da ma shi ne ke jan ragamar tawagar na riƙon-ƙwarya tun bayan da ɗan ƙasar Portugal Jose Piseiro ya ajiye aikin bayan kammala gasar Kofin Afirka a Ivory Coast.

Da yake magana yayin gabatar da shi a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja, Ministan Wasanni John Enoh ya nemi NFF ta bai wa tsoohon ɗan wasan gefen dukkan taimakon da yake buƙata don ya yi nasara.

"Abin alfahari ne gabatar da ni a matsayin kocin Super Eagles, godiya ta musamman ga NFF, da ma'aikatar wasanni, da kuma 'yan Najeriya da suka amince da ni," in ji Finidi cikin saƙon da ya wallafa a X.

Ya ƙara da cewa "aikin babba ne amma da goyon bayan 'yan Najeriya za mu tsallake duk wani ƙalubale kuma mu sa ƙasarmu alfahari".

Finidi zai fara wasansa da Afirka ta Kudu ranar 5 ga watan Yuni, sannan ya kara da Benin ranar 8 ga watan a wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya.

No comments