Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban NILEST Ya Bada Shawarar Yadda Za A Bunkasa Masana'antu Da Gaggawa A Nijeriya

Daga Bello Hamza, Zariya Babban Darakta kuma shugaban Cibiyar Fasahar Fata da kimiyya ta Nijeriya (NILEST) dake Zariya, Farfesa MK Yakubu ya...


Daga Bello Hamza, Zariya

Babban Darakta kuma shugaban Cibiyar Fasahar Fata da kimiyya ta Nijeriya (NILEST) dake Zariya, Farfesa MK Yakubu ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, masu bincike, masana'antu, masu saka hannun jari, ma'aikatun gwamnati da sauran hukumomin da ke Zariya da su samar da kyakkyawar alaka da hadin gwiwar da za ta haifar da habaka masana’antun masarautar Zazzau da jihar Kaduna da ma Nijeriya baki daya cikin hanzari.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabinsa a wajen rufe taron kasuwanci da saka hannun jari na kasa na Zazzau (ZANETIS) a ranar Asabar filin gasar tsere a Zariya wato Zaria Race Course, ya kara da cewa taron an shirya shi ne domin baje kolin zuba jari a harkar noma da ayyukan haÉ—in gwiwa na gona domin bunkasa haÉ—in gwiwa tare da cibiyar binciken fata domin kafa daidaitattun masana'antar takalmi da haÉ“aka kayayyakin fata. A don haka ya kara da cewa, taron zai kuma ba da dama ga bayyana ra'ayoyi daban-daban domin raya sabbin harkokin kasuwanci da masana'antu. 

Ya kara da cewa, “Lokaci ya wuce da satifiket kadai ya isa ya kawo wa mutum abinci. Wannan taron ya assasa yin kira ne ga matasanmu da su rungumi kirkire-kirkire, su bunkasa kaifin tunaninsu kuma su kasance cikin shirin yin gogayya da sauran kasashen duniya. Wane ne ya mallaki biranenmu da suka yi fice ta fuskacin kasuwanci a halin yanzu? Tabbas, ba wadanda suka fi kowa yawan takardun karatu bane. ÆŠaya daga cikin manufofin wannan taron shi ne gwama karatu da kuma Æ™warewa, bincike tare da kuma kasuwanci da aiki tukuru tare da tasiri."

A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Zazzau Dr Ahmed Nuhu Bamall wanda Hakimin Gubuchi, Alhaji Dakta Bello Lawal ya wakilce shi ya yi alkawarin bai wa taron duk wata hadin kai da yake da bukata wajen ganin ya kai ga cimma burin bunkasa masana’antu.

Masana’antu da manyan cibiyoyi da dama ne dake Zariya da kewaye suka halarci taron na kwanaki 10.


No comments