Daga Awwal Umar Kontagora Ƙungiyar Horas da aikin Hajj da Umrah ta Nijeriya ta jihar Neja ta hori mambobinta da kara jajircewa w...
Daga Awwal Umar Kontagora
Ƙungiyar Horas da aikin Hajj da Umrah ta Nijeriya ta jihar Neja ta hori mambobinta da kara jajircewa wajen gudanar da ayyukan horar da maniyyata aikin hajji da masu aikin Umrah.
Jami'in yada labaran kungiyar ta jihar Neja, Muhammad Alhaji Liman yayi kiran a babban filin tashin jiragen sama da ke minna lokacin da kungiyar ke bankwana da maniyyatan jihar.
Jami'in yace maniyyata zasu aikin hajjin ne kamar makafi ba yan jagora, amma muna kiransu da babban murya da su zama yan kasa na gari masu bin dokoki da kyautata mu'amalarsu dan samun damar da aikin Hajji makabuliya.
Yace kamar yadda muka saba a kowace shekara, muna hada hannu da hukumar jin dadin maniyyata wajen sanin dokoki da gyare gyaren da ake samu, ko a wannan shekarar mun dora a inda muke.
Muna da sama da malamai dubu daya da ke gudanar da ayyuka a dukkanin kananan hukumomin jihar nan karkashin wannan kungiya kuma ba malami daya da ya samu damar tafiya tare da maniyyatan jiha.
Wannan mun fahimci wata jarabawa ce ba haka muka so ba, amma tunda hakan ya faru a ganawar mu da maniyyatan jiha, shugaban kungiya ta jiha, Sheikh Muhammadu Liman Masha'Allahu ya jawo hankalin maniyyatan da su jajirce wajen yin aiki da koyarwar da suka samu a lokacin horarwa da suka samu idan sun sauka kasa mai tsarki.
Muna da yakinin kasancewar wannan gwamnatin yanzu ta shigo kuma akwai ayyuka da dama a gabanta. Amma muna fatan nan gaba gwamnatin jiha za ta fahimci muhimmancin tafiya da malamai domin ayyukan jami'an hukumar jin dadin maniyyata daban, ayyukan malamai daban kuma kowani maniyyaci yana bukatar malamin da ke jin harshen sa wajen samun fatawa akan abubuwan da bai fahimta ba a lokacin gudanar da Ibadah.
Jami'in ya shawarci malamai mambobin kungiyar da kar su yi sanyin guiwa wajen cigaba da wannan aikin alheri, domin hanya ta alheri wanda yana daga cikin ayyukan malamai karantarwa da horar da al'umma hanyar aiwatar da Ibadah karbabbiya.
Kungiyar ta yabawa hukumar jin dadin alhazai ta jiha, sassan hukumar da ke yankunan kananan hukumomi musamman wajen hadin kai da goyon baya wajen horas da maniyyatan jihar Neja.
Muhammad Alhaji Liman yace sakamakon irin ayyukan kungiyar nan, jihar Neja samu lambar yabo da dama a shekarun baya daga hukumomin kasar Saudiya na yin jinjina ga maniyyatan jihar Neja wajen nuna da'a da kiyaye dokokin kasar a lokacin gudanar da ayyukan Hajji.
Hajj and Umrah Trainers Association of Nigeria ta jihar Neja ta alwashin cigaba da yin aiki tukuru wajen karantarwa da horas da maniyyatan jiha a kowace shekara dan ganin maniyyatan jihar sun cigaba da samun damar yin Ibadah karbabbiya.
Jami'in ya yabawa malaman da suke gudanar da wannan muhimmin aikin ganin kasancewar tun fara kafa wannan kungiyar suke gudanar da ayyukansu ba tare da neman gudunmawa ko daukar nauyi daga wani ba, maganar gaskiya dole mu yabawa malamai, duk lokacin da uwar kungiya ta jiha ta nemi ganawa da malamai mambobinta suke daukar nauyin kan su na zuwa da dawo da masauki a minna fadar gwamnatin jiha, haka duk lokacin da aka maganar aikin hajji ya taso ko umrah sukan bar ayyukan da ke gaban su da harkokinsu na yau da kullun dan ganin maniyyata sun samu horo ta yadda zasu samu damar gudanar da Ibadah karbabbiya.
No comments