Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar mata musulmi wato FOMWAN ta tallafawa mata masu kananan sana'o'i da jari dan karfafa guiwarsu aka...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar mata musulmi wato FOMWAN ta tallafawa mata masu kananan sana'o'i da jari dan karfafa guiwarsu akan cigaba da sana'o'insu. Da ktake karin haske ga manema labarai, jagorar kungiyar, Amirah Hauwa Kulu Abdullahi Wando, tace tallafin yazo ne a daidai lokacin da kungiyar ta ware dan tunawa da kafuwarta a Nijeriya, wanda aka kafa ta cikin watan June na shekarar 1985.
Tace bayan wannan tallafin a jiya juma'a sun ziyarci babban asibitin gwamnati da ke minna inda suka bada tallafi ga mata da ke jinya a asibitin. Yau kuma sun shirya taron wayar da kan mata kan muhimmancin riko da sana'a wanda kwararren dan gwagwarmayar wayar da kan al'umma masu kananan sana'o',i, Dr. Abubakar Abu Ahmad Gwada ya gabatar da kasida.
Kadidar ta bana mai taken "Tallafawa iyali dan rage kuncin rayuwa ta hanyar taimakon kai wajen riko da sana'a. Ya shawarci matan da su tashi tsaye wajen riko da sana'a da samar da dubarun dorewarsu akkkai".
Dr. Abubakar Gwada, ya lalubo hanyoyin da iyalai zasu dogara da kafarsu wajen riko da sana'a da nusar yara masu tasowa zasu iya fuskantar duk wani kalubalen rayuwa da zai riske su a gaba.
Kungiyar ta bayyana cewar ta horar da yaran tsangayu da dama sana'o'in hannu wanda ya kunshi dunki, kafinta, gyarar wayar salula, sabulai da man shafawa saboda kudurinta na yaki da barace barace.
Hajiya Aishatu Ahmed Lemu daya daga cikin masu tallafawa kungiyar ta jawo hankalin iyaye mata akan kaucewa yawon barace barace da maula a gidajen masu hannu da shuni.
Tace duk wanda ya cire kasala ya tsaya da kafarsa zai zama abin alfahari a cikin al'umma. Yau gwamnati ba ta iya baiwa kowa aiki, amma hakkin kowani dan adam ne ya samarwa kan sa hanyar dogaro a rayuwarsa, wannan hanyar itace roko da sana'a kamar yadda addinin musulunci ya nusar da mu.
Farfesa Halima Shehi, farfesarhar harshen turanci, tace bada wannan tallafin na nufin gamsuwa da tsayuwar mata akan tabbatar da rayuwarsu ta inganta. Dan haka ta jawo hankalin su akan anfani da shawarwarin da mai gabatar kasida ya bayar ta haka ne kananan sana'o'i zasu bunkasa ya zama al'umma ta cigaba da bunkasa, kuma iyalai sun samu sauki akan radadin kuncin rayuwar da ake ciki yanzu.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci dakin taron a makarantar FOMWAN da ke cibiyar yada addini musulunci (Islamic Education Trust) na marigayi Sheikh Ahmed Lemu da ke minna, sun hada Farfesa Halima Shehu, sai Hajiya Aishatu Ahmed Lemu da jagorar kungiyar Amirah Hauwa Kuku Abdullahi Wanda, tare da wakilcin sauran kungiyoyin mata musulmi da suka hada da FOMWAN, NASFAT da wakilcin wasu kungiyoyi.
Zuwa yanzu dai FOMWAN a jihar Neja na daukar dawainiyar karatun yara marayu da marasa karfi a makarantu masu zaman kan su da cikin garin minna da babban birnin tarayyar kasar nan Abuja.
No comments