Daga Abdullahi Musa Makka Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga mazauna jihar Sakkwato da su dauki matakan kariya tun kafin ambaliy...
Daga Abdullahi Musa Makka
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga mazauna jihar Sakkwato da su dauki matakan kariya tun kafin ambaliya ta afku, kamar yadda Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta yi hasashe.
Sanatan ya bayyana hakan ne bayan
kammala sallar Idi a gidansa da ke Gawon Nama, inda ya karbi bakuncin manyan
baki da kuma sauran al’umma.
NiMET ta yi gargadi a cikin Hasashen
Yanayin Shekara ta 2025 cewa za a fuskanci ruwan sama mai yawa da kuma yiwuwar
ambaliya a wasu jihohi, ciki har da Sakkwato. Hukumar ta kuma bayyana damuwa
kan yaduwar cututtukan da ke da nasaba da ruwa kamar kwalera, musamman a
wuraren da ke da matsalolin tsafta.
A cewar NiMET, jihohin Arewa da suka
hada da Sakkwato, Katsina, Zamfara, Kano, Jigawa, Yobe da Borno za su fuskanci
ruwan sama a tsawon kwanaki 110 zuwa 150 a bana.
Sanata Wamakko, wanda ya taba
fuskantar mummunar ambaliya a shekarar 2010 lokacin da yake Gwamnan Jihar
Sakkwato, ya bayyana muhimmancin shiryawa tun da wuri. Ya bukaci jama’a da ke
zaune kusa da koguna da su matsa daga wuraren, ko su tabbatar da cewa hanyoyin
ruwa a bude suke domin ruwa ya rika gudana ba tare da cikas ba.
“Ya kamata mu dauki wannan lamari da
muhimmanci. Na shaida irin barnar da ambaliya ke yi. Kowa ya kula da hasashen
NiMET ya kuma dauki matakin da ya dace domin kare rayuka da dukiyoyi,” in ji
Wamakko.
Sanatan ya kuma gode wa al’umma bisa
addu’o’insu da goyon baya da suke bai wa gwamnati. A wajen taron, Malam Nafi’u
Malami Dan Haja ya jagoranci addu’a ta musamman domin zaman lafiya da daurewar tsaro.
Taron ya samu halartar fitattun
mutane da suka hada da Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari
Dingyadi; karamin Ministan Ayyuka, Barista Bello Muhammad Goronyo; da tsohon
Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Chuso Abdullahi Dattijo.
Wannan kira na Sanata Wamakko na zuwa
ne a wani lokaci mai matukar muhimmanci a yayin da al’ummomi ke shirin
fuskantar damina da ake sa ran za ta kawo kalubale ga ababen more rayuwa da daukar
matakan gaggawa a fadin kasar.
No comments