Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga al'ummar musulmi da su kara kaimi wajen ayyukan alheri da neman kusanci ga Allah ta hanyar raya ...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga al'ummar musulmi da su kara kaimi wajen ayyukan alheri da neman kusanci ga Allah ta hanyar raya kwanakin goman karshen Zul-Hajj. Sheikh Muhammadu Liman Masha'Allahu shugaban kungiyar malamai masu fadakar da Mahajjata da masu aikin Umrah na kasa reshen jihar Neja ne yayi kiran a lokacin kaddamar da wata kasida dan fadakar da al'ummar musulmi muhimmancin raya kwanaki goma na Zul-Hajji da wadanda layyah ya fada kan su.
Masha'Allahu, yace akwai zikirkiru da Manzon Allah ( S. A. W) ya koyar da mu al'umma su kusanci malamai dan sanin wadannan zikirkirun, ita layyah sunna ce ba wajiba ba. Bai halitta mutum ya wajabta ma wani mai arziki cewar dole sai ya ba shi abin layyah, domin bayarwa sadaka ce ga wanda yayi niyyah.
Hakan kuma ba shi zai hanawa masu arziki taimakawa mabukata ba musamman a irin wannan lokacin da al'umma ke fama. Ya halatta idan kana da hali ka sai rago ko akuya, saniya ko rakumi dan raya wannan sunnar ta manzon tsira ka rabawa wadanda Allah ya ciyar da su dan yankawa.
Amma a guji riya, domin ita riya tana rusa duk wani aikin alheri, wanda ya sai abin layyarsa me ye fa'idar daukarsa hoto dan yadawa a yanar gizo har anbata kudin da aka saye, wajen wa ka ke neman ladar, shin kana wannan dabi'ar ne dan al'umma su gani su yaba, ko kuwa ka yi ne dan Allah da samun sakamako a wajen Allah, to al'umma ku kiyaye duk wani abinda zai rusa ayyukan ku na alheri.
Wanda Allah ya baiwa dama yayi yanka, shari'a ta tsara mai yadda zai yi, a nemi malamai dan karin bayani, wanda kuma bai samu dama ba, kar ya daga hankalinsa domin Manzon Allah yayi mai tun yana raye.
Akwai bukatar azumi daga ranar daya ga watan Zul-Hajj har zuwa tara ga wata ga wanda bai samu damar zuwa aikin Hajji ba, ranar goma ga wata an so mutum ya kame bakin sa har saukowa daga sallar Idi, sai ya fara bude baki daga abin layyarsa da ya yanka.
Akwai zikirkiru da ake son yawaitawa, akwai kabarbaru tun daga barin gida har zuwa masallacin Idi, akwai saba hanyar zuwa da dawo wa sallar Idi wadannan dukkansu an so ga musulmi da su lizimce su, saboda falalar da suke cikinsu.
Amma ba wajibi ba ne ga musulmi ya zauna jiran wani mai arziki akan tilas ya ba shi abinda layyah, wanda in bai ba shi ba zai zama mai laifi a gare shi. Allah ya shimfida kasa ya kuma watsa arziki a cikinta, idan ka tashi ka jajirce idan ba ka samu ba yau, gobe Allah na iya ba ka, amma ba ka zauna jiran dole sai wani ya baka ba.
Dukkanin shugabanni da suka jagoranci addinin musulunci mun ga irin jajircewar da suka yi wajen yiwa addini hidima da arzikin da Allah ya ba su, to kai kama ka jajirce ka samu dan samun matsayi a wajen Allah.
Malamin, yayi kira ga gwamnati da ta ji tsoron Allah ta sauke nauyin da ke kan ta wajen samun hanyoyin saukaka tsadar rayuwa da al'umma ke ciki, jama'a na neman kulawar gwamnati, kamar yadda gwamnati ke neman goyon bayan talakawan kasa.
Matsalar tsaro, rashawa, ta'addanci duk sun taimaka wajen karuwar talauci a kasar nan, manoma na tsoron shiga daji, yan kasuwa na tsoron bin hanyoyi, yayin da duk wata bukata indai ta hada da gwamnati sai dogon hannu ko wanda yake da wani makusanci mai karfi, wadannan abubuwa ne da ke bukatar kulawar gwamnati da gaggawa.
Sheikh Masha'Allah ya gabatar da addu'o'i na musamman ga kasa na zaman lafiya da kawo karshen rashin tsaro, da addu'o'i ga shugabanni dan samun kwarin guiwar sauke nauyin da ke kan su.
No comments