Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Leburori Masu Haƙar Ma'adanai Ta Nesanta Kan Ta Da Haɗarin Ruftawar Ƙasa A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Shugaban kungiyar leburori masu hakar ma'adanan kasa ( Nigeria Union of mines workers) reshen jiha...

Daga Awwal Umar Kontagora

Shugaban kungiyar leburori masu hakar ma'adanan kasa ( Nigeria Union of mines workers) reshen jihar Neja, Comr. Musa Adamu Nasko ya nesanta kungiyarsu da hadarin ruftawar kasa da ya kai ga salwantar leburori sama da talatin yankin Farin-doki na karamar hukumar Shiroro.
Nasko yace wadanda abin ya shafa ma ba yan ma'adini ba ne, suna aiki ne karkashin wani kamfani wanda shi kan shi mai kamfanin ya nesanta kan shi da mu.

Domin shekaru hudu da suka wuce ya kai mu high court saboda mun nemi leburorinsa su yi rajista da mu, ganin mafi yawan leburorin membobin mu ne ya kore su daga kamfanin.

Bayan wannan hukunci ya koma dauko leburorin tifa masu jidar kasa yana aiki da su, wanda jami'an tsaro sun san gaskiyar lamarin, saboda haka wannan abin sai dai mu tausayawa rayuwa amma kungiyar NUMW reshen jihar Neja abin bai shafe ta ba.

Abinda NUMW ta sani shi ne gwamnatin Neja ta kafa dokar dakatar da hakar ma'adani a jihar nan, kuma tuni kungiyar mu ta bi sahon bin dokar, wanda duk ka gani a daji da sunan dan ma'adani yana aiki to ina mai tabbatar maka cewar ba memban mu ba ne.

Ina kiran gwamnatin jiha da babban murya da ma'aikatar kula da ma'adanai na jihar Neja da su hada kai da mu gwamnati ta ba mu dama za mu tabbatar mun shiga lungu da sako wajen lalubo duk wani dan ma'adani da ke aiki ba bisa ka'ida ba.

NUMW kungiya ce wadda ke hadaka da kungiyar kwadago ta kasa, kuma amince da umurnin gwamnatin jiha ne saboda kasancewar mu yan kasa masu biyayya. Don haka ina kara kira ga duk wani mamban mu ya kara hakuri akan wannan matsayin da yardar Allah za a samu mafita, amma har gobe kungiya ba ta amince wani lebura ya shiga rami dan cigaba da hakar ma'adani ba.

Binciken wakilin mu ya gano cewar akwai kamfanoni da dama da aikin hakar ma'adanai a jihar Neja masu zaman kan su wadanda ke samun daurin gindin wasu manya duk da dokar dakatarwar da gwamnatin Neja tayi.

No comments