Wakilan Majalisar Dokokin Amurka 16 sun roƙi Shugaba Joe Biden da ya shiga tsakani don ganin an saki babban jami’in kamfanin hada-hadar kuɗi...
Wakilan Majalisar Dokokin Amurka 16 sun roƙi Shugaba Joe Biden da ya shiga tsakani don ganin an saki babban jami’in kamfanin hada-hadar kuɗin intanet, Binance, Tigran Gambaryan, wanda ake tsare da shi a Najeriya tun watan Fabarairu.
Gwamnatin Najeriya ta kama Gambaryan inda yake fuskantar tuhumar ƙin biyan haraji da kuma yadda kamfanin ke taimaka wa masu hada-hada wajen kauce wa haraji.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ƴan majalisar sun ce a matsayin Gambaryan na ɗan Amurka, bai dace gwamnatin wata ƙasa ta tsare shi ta hanyar da ba ta dace ba, har ma a riƙa gallaza masa.
Ƴan majalisar sun kuma bayyana damuwarsu kan lafiyarsa.
"Dole ne mu ɗauki mataki cikin gaggawa kafin lokaci ya ƙure," in ji 'yan majalisar dokoki, ciki har da shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar wakilai, Michael T. McCaul, R-Texas.
Sun sake nanata cewa Gambaryan, babban jami'in kula da harkokin kuɗi na Binance, "an tsare shi bisa kuskure" tun daga ƙarshen watan Fabarairu bayan da ya bayar da buƙatar gwamnatin Najeriya don tattaunawa game da kasuwancin kuɗin Kirifto a ƙasar.
'Yan majalisar sun ce suna buƙatar taimakon gwamnatin Biden domin mayar da Gambaryan ƙasarsa.
No comments