Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Alhaji Bello Dan Agwai Ya Zama San-Turakin Dnata

Daga Abubakar Musa, Zariya A ranar 29 ne mai martaba sarkin Dnata Injiniya Jemes Bitrus ya naɗa Alhaji Bello Dan Agwai a matsayin San-Turaki...



Daga Abubakar Musa, Zariya

A ranar 29 ne mai martaba sarkin Dnata Injiniya Jemes Bitrus ya naɗa Alhaji Bello Dan Agwai a matsayin San-Turakin ƙasar Dnata dake karamar hukumar Kagarko jihar Kaduna.

Wakilanmu ya sami zuwa wajan naɗin sarautar da ya gudana a garin Tafa dake karamar hukumar Kagarko jihar Kaduna

Bayan bakin sarakuna yan siyasar dake a wannan shiryar sun gama halartar wajan da aka gabatar da bukin naɗin kungiyoyi masu zaman kansu sun gabatar da wasanni dake nuna farin cikin ga wannan naɗi.

Bayan kammala naɗin Alhaji Bello a matsayin San-Turaki ya zanta da manema labarai game da sarautar da aka bashi.

"Nayi matukar farin ciki game da wannan karamcin dana samu kuma zan karance mai adalci wajan kare jama'ar masarautana"

Ya ƙara da cewa zamu zama jakadu na kwarai da yardar Allah kuma yayi kira da dukkan sauran mutane masu rawunna dasu zo su haɗa kai don yiwa masarautar Dnata ci gaba

Ya kuma yi godiya ga dukkan jama'ar da suka bada lokaci wajan tabbatar wannan sha'ani yayi fatan Allah ya mayar da kowa gida lafiya.

Shima Sarkin Injiniya Jemes Bitrus a nasa jawabin ya bayyana cewa dukkanin wanda aka naɗa an naɗasu ne bisa cancanta.

Kuma ya yaba masu game da gudunmawar da suke baiwa masarautar tasu yace haka akeso.

Ƙarshe Sarkin yayi fatan dukkan wanda suka zo taron Allah ya koma dasu garuruwansu lafiya.


No comments