Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Dnata Ya Yi Bikin Naɗin Wasu Muƙamai A Masarautarsa

Daga Idris Umar, Zariya  Mai martaba sarkin Dnata HRH Injiniya Jemes Bitrus Abwaminajiya Sa'dnatayi na (l) dake ƙaramar Hukumar Kagarko ...


Daga Idris Umar, Zariya 

Mai martaba sarkin Dnata HRH Injiniya Jemes Bitrus Abwaminajiya Sa'dnatayi na (l) dake ƙaramar Hukumar Kagarko ta jihar Kaduna ya naɗa wasu muhimman mutane a masarautarsa bisa cancantarsu a satin da ya gabata.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa dake garin Tafa ya ce,masarautar ta Dnata masaurata ce mai albarka wacce ke da mutane masu ƙokari da girmama juna, ya ce, bisa haka ne ya zaɓi wasu don su zama waƙilai a cikin al'ummarsa.

Sarki ya yi godiya matuƙa bisa yadda jama'a ke bashi goyan baya a kowani lokaci ya ce hakan na ba shi sha'awa da har zai ba su tukuici da matsayi a majalisar tasa.

Bayan haka sarkin ya yi wa dukkan jama'ar ƙasar na sa fatan alheri bisa girma da suke bai wa masarautar tare da kare mutuncinta.

A cikin wanda ya bai wa wannan rawuna akwai Alhaji Sama'ila Gano wanda shi ne aka naɗa a matsayin Barwan Dnata sai Alhaji Yusuf Ƙarda wanda aka naɗa shi a matsayin  Sarki Bakan Dnata sai Malam Abdul-Aziz mai (Aruntumau) shi aka naɗa a matsayin Sarkin Dawan Dnata sai Alhaji Audun Zato shi ne aka naɗa a matsayin Ɗan Iyan Dnata sai Alhaji Bello Dan Agwai wanda aka naɗa shi a matsayin Santurakin Dnata akwai mutane da dama cikin wanda sarkin ya ya yi masu karamci da ba su rawanin wakilci a wannan masarauta.

Sarkin ya yi yabo ga mai girma Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, bisa kokarin da yake yi a ɓangarori daban daban a faɗin jihar.

Kuma ya yabawa dukkan 'yan siyasar jihar Kaduna da jami'an tsaro bisa kokarin da suke yi wajen gudanar da shugabanci mai tsafta da kare mutuncin al'umma da al'adunsu da addinin su.

Jama'a ƙasar sun yi shaida tare da yin yabon ga matsayin mutanen da aka ƙarrama cewa mutane masu rikon amana da sanin ya kamata a cikin al'ummar ƙasar ta Dnata dake karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna

An yi nadin lafiya an tashi lafiya.

No comments